Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta bayyana dalilan da suka sa aka tura ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ...
Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta bayyana dalilan da suka sa aka tura ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, zuwa gidan yarin Kuje a Abuja — duk da cewa an riga an ba shi beli daga kotu.
An kama Sowore ne a ranar Alhamis bisa zargin tayar da hankalin jama’a da yin zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow duk da gargadin da rundunar ta bayar tun da farko.
An gurfanar da shi tare da wasu mutane 12 a gaban kotun majistare ta Kuje a ranar Juma’a, inda suka musanta laifukan da ake tuhumar su da su. Kotu ta ba shi beli na naira ₦500,000 tare da masu ruwa biyu, kuma lauyoyinsa suka fara kammala sharuddan belin lokacin da abin ya faru.
Sai dai jim kaɗan bayan belin, wasu ‘yan sanda sama da 50 suka mamaye harabar kotun, suka yi amfani da ƙarfi wajen cafke Sowore, suka ja shi da karfi zuwa gidan yarin Kuje — abin da ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin lauyoyinsa da jami’an tsaro.
Deji Adeyanju, wani ɗan gwagwarmaya, ya bayyana cewa jami’an sun ƙi nuna takardar da suka ce umarnin kotu ne, sai dai kawai ɗaya daga cikinsu ya ɗaga ta na ɗan lokaci sannan ya ɓoye.
“Mun nemi mu duba takardar amma ya ƙi, sai ya ce kawai za su tafi Kuje Prison. Jami’an sun yi masa duka, sun yayyaga rigarsa kafin su tafi da shi,” inji Adeyanju.
Sai dai da yake mayar da martani a shafinsa na X (Twitter), mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Benjamin Hundeyin, ya ce an bi doka ƙwarai, domin duk wanda aka ba shi beli zai ci gaba da kasancewa a tsare har sai an kammala sharuddan belin nasa.
Hundeyin ya bayyana cewa “Kotu tana bayar da beli ne da sharadi — har sai an cika ka’idojin belin, wanda ake zargi zai ci gaba da kasancewa a tsare. Idan takardar umarnin ta nuna cewa a mika shi gidan gyaran hali, to aikin ‘yan sanda ne su kai shi can, inda za a ci gaba da aiwatar da belinsa.”
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro suna da damar yin amfani da ƙarfi “matsakaicin da ya dace” wajen aiwatar da umarnin kotu.
A halin yanzu, Sowore da wasu mutum 12 da aka kama tare da shi suna cigaba da kasancewa a gidan yarin Kuje yayin da ake kammala sharuɗɗan belinsu.

No comments