Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Majalisar Dokoki Ta Amince A Ƙirƙiro Jihohi Shida A Nijeriya

Kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa da ta Wakilan Nijeriya kan yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar garambawul ya amince da a ƙirƙiro jiho...



Kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa da ta Wakilan Nijeriya kan yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar garambawul ya amince da a ƙirƙiro jihohi guda shida.

Wannan na cikin matsayar da aka cimmawa a ƙarshen taron ƙara wa juna sani na kwana biyu, wanda mataimakin majalisar dattawa Sanata Barau I. Jibrin da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu suka jagoranta a jihar Legas.

Kwamitin ya tattauna ne kan buƙatu guda 69, ciki har da buƙatar ƙirƙirar jihohi 55 da buƙatar a ƙirƙirar ƙananan hukumomin 278.

A game da buƙatar ƙirƙirar jihohi 55 da aka gabatar a ranar Asabar, kwamitin ya amince da ƙirƙirar jihohi guda shida a duk shiyoyin ƙasar guda shida.

Idan aka amince da ƙirƙirar sababbin jihohi, Nijeriya za ta zama tana da jihohi 42 ke nan.

No comments