Daga Hussaini Yero, Funtua A ranar Alhamis da ta gabata ne Uwargidan Shugaban Ƙasa Sanata Remi Tinibu ta ƙaddamar na ɗakin karatu na E-lear...
Daga Hussaini Yero, Funtua
A ranar Alhamis da ta gabata ne Uwargidan Shugaban Ƙasa Sanata Remi Tinibu ta ƙaddamar na ɗakin karatu na E-learning A Gusau babban Birnin Jihar Zamfara.
Da ta ke wakiltatar Sanata Remi Tinibu, Uwargidan Gwamnan Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta yaba wa shirin Ilimi na zamani na Gwamnatin Tarayya, inda ta ce zai bunƙasa ci gaban ƙasa baki ɗaya.
Hurriya Lawal ta yaba da ƙaddamar da ɗakin karatun na zamani na E-Learning wanda aka gudanar a Gusau, wanda Zamfara na ɗaya daga cikin jihohi goma da aka zaba domin cin gajiyar shirin a faɗin ƙasar nan ƙarƙashin shirin Renewed Hope Initiative (RHI) tare da haɗin gwiwar Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA)
Ta ce aikin ba wai na fasaha da na’ura mai kwakwalwa ba ne kawai, yana da nufin karfafa wa matasanmu karfi, tare da bude sabbin kofofin ilimi da kirkire-kirkiren zamani ga al’ummar Zamfara da sauran su.
Ta hanyar wannan ɗakin karatu na E-library, ɗalibai, malamai, masu bincike da sauran jama'a za su sami damar yin amfani da duniyar bayanai, da dama a hannunsu.
A cewarta, shirin Renewed Hope Initiative, wanda mahaifiyarmu masoyiyar Kasar nan, Sanata Oluremi Tinubu ta jagoranta, ita ce manufa ta tallafawa ilimi, kirkire-kirkire, da ci gaban zamantakewa. Wannan ɗakin karatu na zamani yana nuna hangen nesa da halinda da aka cika.
“Saboda haka, ina yaba wa ma’aikatar sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin ta tarayya da Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA) bisa gudanar da wannan aiki da kyau. Ina kuma matukar godiya ga maigidana, Gwamna Dauda Lawal da daukacin gwamnatinsa bisa jajircewarsu na inganta ilimi a Zamfara.
A nasa jawabin Babban Daraktan Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA) Kashifu Inuwa, ya buƙaci al’ummar Zamfara musamman ɗalibai da malamai da su yi kyakkyawan amfani da wannan wurin.
Shi ma da yake jawabi Kwamishinan ilimi na kimiyya da fasaha, Mallam Wadatau Madawaki, ya ce wannan aiki ya yi dai dai da tunanin gwamna Dauda Lawal wanda tuni ya ayyana dokar ta baci akan ilimi a kan hawan sa kan karagar mulki.Tun daga wannan lokacin, fannin ya sami gagarumin sauyi da nufin farfado da fannin Ilimi daban -daban.
Kwamishinan, wanda Babbar Sakatariya a ma'aikatar ta wakilta, Maryam Shantali ta ce a madadin ma’aikatar da kuma al’ummar Zamfara, “Ina miƙa godiyarmu ga Uwargidan shugaban Najeriya Sanata Oluremi Tinubu, bisa shigar da Zamfara cikin wannan kyakkyawan shiri.
"Muna ba ku tabbacin cewa za a yi amfani da wannan wurin ga ɗalibanmu, malamanmu, da masu bincike".


No comments