Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

SABON TSARIN RITAYAR MANYAN JAMI'AN SOJI: Tsofaffin Hafsoshin Soji Za Su Tafi Da Motocin Alfarma Da Dala 60,000

Sababbin ƙa’idojin ritayar Hafsoshin tsaro da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da su sun bayyana irin gagarumin alherin da tsofaffi...



Sababbin ƙa’idojin ritayar Hafsoshin tsaro da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da su sun bayyana irin gagarumin alherin da tsofaffin manyan Hafsoshin soji za su samu bayan barin aiki.

A cewar takardar “Harmonised Terms and Conditions of Service (HTACOS) 2024”, wadda Tinubu ya sanya wa hannu, tsohon Hafsan Tsaron Ƙasa da sauran Hafsoshin rundunonin soji da aka yi wa ritaya za su tafi da motar kariya daga harsashi (bulletproof SUV) da kuma motar Prado Jeep, ko makamancin su, wanda za a riƙa gyarawa da sauya su duk bayan shekaru huɗu.

Haka kuma, kowane ɗayan su zai samu Dalar Amurka $20,000 a kowace shekara domin kiwon lafiya, yayin da sauran hidimomin su za su ci gaba da kasancewa ƙarƙashin kulawar rundunonin da suka fito.

Tinubu ya amince da cire tsofaffin hsafsoshin soji a ranar Asabar, inda aka maye gurbinsu da sabbi:

Janar Olufemi Oluyede — sabon Shugaban Tsaron Ƙasa,

Manjo Janar W. Shaibu — sabon Shugaban Rundunar Soja,

Air Vice Marshal S. K. Aneke — sabon Shugaban Rundunar Sama,

Rear Admiral I. Abbas — sabon Shugaban Rundunar Ruwa.

A cikin tanadin ritayar, an fayyace cewa kowane tsohon babban hafsan zai kuma samu:

Ɗakunan aiki da sojoji da ma’aikata (cooks, stewards, gardener),

Direbobi uku,

Sojoji tara masu gadi,

Dogarin soja,

Mai taimako na musamman,

Da izinin riƙe makaman kansa har zuwa bayan mutuwa.

Haka kuma, za su riƙa samun cikakken magani a gida da ƙasashen waje.

Ga waɗanda ke da muƙamin Lieutenant-General, su kuma za su tafi da motar Toyota Hilux da Land Cruiser, tare da ma’aikata shida da kuɗin magani har zuwa $20,000 a shekara.

Manyan Janar (Major-General) za su samu mota ɗaya, ma’aikata biyar, da kuɗin magani har zuwa $15,000 a shekara.

Ƙananan Janar (Brigadier-General) kuma za su samu mota ɗaya da kuɗin magani $10,000 a shekara.

Wani binciken jaridar LEADERSHIP ya nuna cewa fiye da janar 60 za su iya yin ritaya a wannan karo, domin sabon Shugaban Sojan Ƙasa yana daga cikin Course 41 na makarantar NDA, wanda hakan ke nufin manyan hafsoshi daga Course 39 da wasu daga 41 za su bar aiki.

Wani tsohon mai ba wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari shawara, Okoi Obono-Obla, ya bayyana wannan sauyi a matsayin “tsarin sabuntawa” da Tinubu ke yi domin ƙarfafa tsaro da gyara tsarin mulkin soji.

Ya ce wannan sauyin “yana nuna kwarewar Tinubu wajen daidaita tasirin siyasa da yankuna domin tabbatar da tsaro da haɗin kai a ƙasa.”

No comments