Daga Hussaini Yero, Funtua Uwargidan gwamnan jihar Zamfara Hajiya Huriyya Dauda Lawal, kuma Sakatariya ta Yaƙi da Cutar Kansar mama ta ƙasa...
Daga Hussaini Yero, Funtua
Uwargidan gwamnan jihar Zamfara Hajiya Huriyya Dauda Lawal, kuma Sakatariya ta Yaƙi da Cutar Kansar mama ta ƙasa, ta ƙaddamar da kamfen wayar da kai akan Cutar Kansar Mama ga ɗalibai Mata 'Yan Sakandire A Gusau babban Birnin Jihar Zamfara.
A jawabin ta, Hajiya Huriyya Dauda ta bayyana farin ciki da kasancewa tare da ɗalibai a yau domin bikin Ranar wayar da kai kan cutar Kansar Mama wadda taken wannan shekara shi ne, Kowacce tafiya na da Muhimmanci,” hakan na tunatar da mu cewa kowacce mace tana da daraja, kuma ta cancanci kulawa, tausayi, da samun dama. Kuma idan muka lura da taken na duniya na bana da ke cewa “haɗin kai na musamman” yana nuna mana cewa duk da bambance-bambancen mu, haɗin kai ne tushen ƙarfin mu .inji Hurriya Lawal ".
"Mu mata musamman a yankunan mu, muna fuskantar kalubale na lafiyar jiki kamar ciwon nono da mahaifa. Saboda haka ina kira gare ku, ku kula da lafiyar ku, ku dinga zuwa gwaji akai-akai, kuma ku ƙarfafa wa mata guiwa, su ma su kula da nasu. Ku dalibain ilimi ne da kuke samu a yau zai taimaka muku wajen ɗaukar sahihan matakai da za su kare lafiyar ku, kuma ku zama haske ga sauran mata a nan gaba.
Huriyya Dauda ta mika godiya ta musamman ga ƙungiyar First Ladies Against Cancer (FLAC), sakamakon jajircewar su wajen faɗakar da al’umma da tallafa wa masu fama da wannan cuta. A matsayina na Uwargidan gwamnan jahar Zamfara kuma Sakatariyarta ƙasa ta ƙungiyar, ina tabbatar muku cewa ofishina zai ci gaba da wayar da kai, shirye-shirye da ƙarfafa mutane wajen gano cutar da wuri, yin gwaje-gwaje, da bin hanyoyi masu tsafta da lafiya.
Bugu da ƙari, ina miƙa godiya ga Maigidana, Mai Girma Gwamnan Jahar Zamfara Dauda Lawal, bisa irin hangen nesa da jajircewar sa wajen inganta harkar lafiya a jahar. Ƙoƙarin sa yana tabbatar da cewa mata, yara, da mabuƙata gaba ɗaya suna samun kulawa ta lafiya mai inganci .; tare da nuna soyayyar shi da kishin jama’ar jahar Zamfara.
A ƙarshe, tayi kira da riƙe wanna sako na yau dan fadakar da iyayenku, ‘yan’uwanku, da abokanku cewa, lafiya ni’imace, ilimi kuwa Garkuwar ne. Mu tashi tsaye tare wajen gina al’umma mai lafiya, wadda babu wanda zai fuskanci cutar Kansa shi kaɗai. Da ilimi, jarumtaka, da haɗin kai, za mu iya hana cutar yadowa da wuri, da magance ta.
Dakta Khadijat tayi bayyana akan illar Cutar Kansar Mama da kuma yadda Ake ganota da maganceta anan take .
Dakta Khadijat tayi cikaken bayani ga Dalibai akan yadda mace zata iya gano Cutar Kansar Mama kuma da Kanta saita garzaya Asibitin dan yin allurar rigakafi.

No comments