Daga Idris Ibrahim, Azare Gwamnatin jihar Bauchi ta sassauta hukucin korar da aka yi wa Hakimin Azare, Alhaji Bashar Kabir Umar, inda maimak...
Daga Idris Ibrahim, Azare
Gwamnatin jihar Bauchi ta sassauta hukucin korar da aka yi wa Hakimin Azare, Alhaji Bashar Kabir Umar, inda maimakon kora kwata-kwata, yanzu an mayar da ita sallama.
Wannan sassauci yana ƙunshe ne cikin wata takarda daga Hukumar kula da Ƙananan Hukumomi ta jihar Bauchi, wacce aka aike wa Alhaji Bashar, mai ɗauke da kwanan wata 29 Oktoba, 2025 tare da sa hannun Nasiru Ibrahim Dewu.
"An umurce ni da in sanar da kai cewa Mai girma Gwamnan jihar Bauchi ya amince da canja korar da aka yi maka a matsayin Hakimi, yanzu hukuncin ya koma sallama daga aiki. Wannan kuwa ya faru ne sakamakon neman gafarar da ka yi, wanda ta sanya aka yi maka wannan rangwame," kamar yadda ya ke ƙunshe a takardar.
Saboda haka bisa wannan ci gaba da aka samu, yanzu an umurci hukumomin da abin ya shafa da su tattara haƙƙoƙin tsohon Hakimin, waɗanda suka haɗa da Fansho da Garatuti don a miƙa masa.
A ƙarshe, Hukumar ta yi kira ga tsohon Hakimin da ya ci gaba da zama jakada na ƙwarai a cikin al'ummar sa.





No comments