Gwamnan na Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya rantsar da sabon Kwamishinan ma'aikatar yaɗa labarai ta jihar Malam Ahmed Maiyaki, wanda zai ...
Gwamnan na Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya rantsar da sabon Kwamishinan ma'aikatar yaɗa labarai ta jihar Malam Ahmed Maiyaki, wanda zai ƙara taimaka wa majalisar Zartarwar Jihar ƙaimi domin sauke nauyin da Allah ya ɗora masu.
Gwamnan ya rantsar da Kwamishinan ne a yayin zaman majalisar zartarwar jihar, wanda ya gudana a ɗakin taro na fadar gwamnatin jihar a yau Talata 21 ga watan Oktobar 2025.
Ahmed Maiyaki, wanda shi ne tsohon Shugaban Hukumar kafafen yaɗa labarai na jihar Kaduna ( KSMC), hakazalika Maiyaki ya kasance tsohon Daraktan yaɗa labarai na tsohon gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero.
Ahmed maiyaki, ya daɗe yana bayar da gudumawa a harkar yaɗa labarai a a faɗin ƙasar nan bayan kasancewar sa tsohon ma'aikaci a sashin Hausa na rediyon Faransa (FRI).
Jihar Kaduna ta kwashe shekaru takwas babu ma'aikatar yaɗa labarai wacce tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ya rufeta, sai bayan lashe zaben Gwamna Uba Sani ya dawo da ma'aikatar wacce aka ɗora wa alhakin kula da yaɗa manufofin gwamnatin jihar.


No comments