Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

BINCIKE: Jihar Kaduna Ta Ƙara Zama Jihar Da Ta Fi Gaskiya Da Riƙon Amana A Nijeriya

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sake bayyana kanta a matsayin jihar da tafi gaskiya da rikon amana a Nijeriya, bayan da ta sake fitowa ta farko a ...


Gwamnatin Jihar Kaduna ta sake bayyana kanta a matsayin jihar da tafi gaskiya da rikon amana a Nijeriya, bayan da ta sake fitowa ta farko a jerin Jihohin da  Wani binciken da (Transparency & Integrity Index) tayi na shekarar 2025.

A wani binciken da  Cibiyar Ingantaccen Bayyanai  da Aminci (CeFTPI) tare da tallafin MacArthur Foundation ta fitar sun bayyana cewa Wannan shi ne karo na biyu a jere da Kaduna ke lashe wannan matsayi, abin da ke kara tabbatar da sunanta a matsayin jihar da ke da gaskiya, amana, da nagartaccen shugabanci.

A cewar rahoton, Kaduna ta samu maki 49.08%, ta zama ta farko a kasa gaba da Kano (46.86%) da Osun (45.97%).

 Haka kuma, jihar ta samu mafi girman maki a fannin dakile cin hanci da rashawa da kashi  (80%), abin da ke nuna tsauraran matakan yaki da cin hanci da rashawa da kuma jajircewarta wajen ingantaccen shugabanci.

Rahoton ya tantance jihohi 36 na Nijeriya bisa fannoni biyar, Bayyana harkokin Kudi  (Fiscal Transparency), buɗaɗɗen Siyan Kaya da  Albarkatun Ma’aikata  tare da Yaki da Cin Hanci  da rashawa da hadin Kan Jama’a.

Kyakkyawan sakamakon da Kaduna ta samu a wadannan fannoni ya nuna tasirin irin jagorancin gyara da Gwamna Uba Sani ke jagoranta, wanda ke ci gaba da gina tubalin nagartaccen mulki da aka kafa a jihar.

Da yake mayar da jawabi  kan wannan ci gaba, Gwamna Uba Sani ya ce: "Gwamnatina ta sanya gaskiya da bayyanawa a gaba a matsayin ginshikin ci gaba mai dorewa. Wannan karramawa daga Cibiyar Bayyanawa  da Aminci ta tabbatar da cewa Jihar Kaduna ba wai kawai tana aiki ba bane , tana yin hakan ne da amana"

"Za mu ci gaba da zurfafa gyare-gyare da  karfafa hadin kan jama’a, tare da tabbatar da cewa kowane kobo an san yadda aka kashe shi.” in ji shi.

Shi ma Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana wannan nasara a matsayin “tabbataccen shaida ta irin gwamnatin da ke samar da sakamako a karkashin Gwamna Uba Sani.”

“A wannan matsayi an same sune   sakamakon manufofi da gyare-gyaren da aka tsara ne domin inganta bayyanawa tare da rage cin hanci, da tabbatar da cewa mulki yana kawo sakamako ga ‘yan kasa. Wannan ya nuna cewa Gwamna Uba Sani yana da imani da" in ji Maiyaki.
 

No comments