Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

ƘARFAFA HULƊA: Kwamishinan Yaɗa Labarai Na Jihar Kaduna Ya Fara Ziyarar Kafofin Sadarwa

A ƙoƙarin da gwamnatin jihar Kaduna ke yi na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da kafafen yaɗa labarai wajen yaƙi da yaɗa labaran...

A ƙoƙarin da gwamnatin jihar Kaduna ke yi na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da kafafen yaɗa labarai wajen yaƙi da yaɗa labaran ƙarya, Kwamishinan Yaɗa Labara na Jihar, Malam Ahmed Maiyaki, ya fara ziyarar aiki zuwa manyan kafafen watsa labarai a jihar.

Ziyarar, wacce ta fara a farkon wannan mako, ta haɗa da ziyarar tashoshin watsa shirye-shirye na gidan Talabijin na ƙasa (NTA), da gidan rediyon  Freedom da DITV/Alheri Rediyo.

A ziyarar, Malam Maiyaki ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Uba Sani tana ganin kafafen watsa labarai a matsayin muhimman abokan hulɗa wajen tantance gaskiya da samar da bayanai ingatattu waje gudanar da mulki mai mayar da hankali kan al’umma.

Maiyaki ya jaddada cewa manufar ziyarar ita ce  ƙarfafa dangantaka tsakanin gwamnati da ma’aikatan kafafen labarai domin tabbatar da cewa jama’a suna samun sahihan bayanai daga amintattun hanyoyi.

Kwamishinan ya kuma tabbatar da aniyar gwamnatin jjhar Kaduna wajen ci gaba da kasancewa a buɗe da kuma yin mu’amala akai-akai da ’yan jarida, yana mai cewa ingantacciyar sadarwa ita ce ginshiƙin gina amincewar al'umma  ga gwamnati.

A nasa bangaren, Daraktan shiyya na NTA, Malam Isyak Abbass, da Daraktan Gudanarwa na rukunnin gidajen radiyon  Freedom , Malam Lawal Mohammed, sun yaba da yunƙurin Kwamishinan, inda suka  bayyana shi a matsayin mataki na ƙara ƙarfafa haɗin kai tsakanin gwamnati jiha da kafafen yaɗa labarai a jihar baki ɗaya.

 

No comments