Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Fasahar AI Ɗin Hukumar CAC Ta Amince Da ‘BokoHaram Hub’ A Matsayin Kamfani

’Yan Nijeriya da dama sun nuna matuƙar damuwa dangane da amincewar da Hukumar yi wa kamfannoi rajista CAC ta amince da yi wa wani kamfani wa...


’Yan Nijeriya da dama sun nuna matuƙar damuwa dangane da amincewar da Hukumar yi wa kamfannoi rajista CAC ta amince da yi wa wani kamfani wai shi ‘BokoHaram Training Hub’ da wani kuma wai shi ‘Nigeria Must Scatter’ da dai sauran wasu kamfanoni masu munanan sanaye a matsayin sunayen kasuwanci, wanda sabuwar manhajar rajista ta Hukumar ta (CAC) ta yi, inda suka zarge ta da ba da fifiko ga tsarin amincewa da sauri ta na'ura mai sarrafa kanta maimakon bin hanya mai inganci da tsaro.

A ranar 1 ga Yuli, 2025, CAC ta qaddamar da wata sabuwar hanyar rajistar mai amfani da bayanan sirri mai suna Intelligent Company Registration Portal (ICRP) 3.0 wanda ya yi alqawarin haɗa kasuwanci cikin mintuna 30.

A cewar hukumar, an ɗauki wannan matakin ne domin a samu sauqin gudanar da harkokin kasuwanci a Nijeriya, musamman ma masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i.

Majiyoyi sun bayyana cewa kwanan nan tsarin ya amince da yin rajistar sunayen kasuwanci kamar "Cibiyar Kai Wa ’Yan Bindiga Abinci", “Cibiyar Horar da Boko Haram”, “Kamfanonin Ƙera Abubuwan Fashe”, da Kamfanonin Watsewar Nijeriya – wanda a da ƙwararrun jami’an CAC za su yi watsi da su nan take.

Wannan lamari ya haifar da damuwa mai tsanani game da haɗarin rashin sa ido a cikin muhimman ayyukan gwamnati.

No comments