Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu, GCFR ya amince da kafa kwamitin da zai shirya gudanar da jana'izar Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhar...
Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu, GCFR ya amince da kafa kwamitin da zai shirya gudanar da jana'izar Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, GCFR a gwamnatance.
Kwamitin wanda Sakataren gwamnatin tarayya, George Alume, CON zai jagoranta, an ɗora masa alhakin tsarawa da gudanar da jan'izar Tsohon Shugaban Ƙasan.
Cikin wata ssnarwa da Daraktan hulɗa da jama'a, Segun Imohiosen ya fitar, ta bayyana cewa Mambobin wannan kwamiti sun haɗa da:
i. Ministan Kuɗi
ii. Ministan kasafi da tsara tattalin arziki
iii. Ministan tsaro
iv Ministan yaɗa labarai da wayar kai
v. Ministan ayyuka
vi. Ministan harkokin cikin gida
vii. Ministan Birnin tarayya
viii. Ministan gidaje da raya birane
ix. Ƙaramin Ministan lafiya da jin daɗin jama'a
x. Ministan al'adu
xi. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro
xii. Babban mashawarci ga shugaban ƙasa a harkokin tsare-tsare da gudanarwa
xiii. Babban mataimaki ga shugaban ƙasa a harkar siyasa da wasu harkoki
xiv. Shugaban 'yan sandan Nijeriya
xv. Shugaban hukumar tsaron farin kaya ta DSS
xvi. Babban Hafsan tsaro na ƙasa
Sannan ofishin babban Sakatare kan al'amuran yau da kullum ne zai kasance matattarar bayanan wannan kwamiti.
Haka kuma, don ƙarin girmamawa ga marigayi Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Shugaba Tinubu ya umurci dukkan ma'aikatun gwamnatin tarayya da su buɗe littafin yin ta'aziyya don ma'aikata su samu damar rubuta ta'aziyyar su na wannan rashi.
Bugu da ƙari, za a buɗe wata rajistar a ma'aikatar kula da ƙasashen wajen, da babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre, Abuja don baƙi 'yan ƙasashen waje da sauran jama'a su samu damar yin ta su ta'aziyyar.
No comments