Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

DA ƊUMU-ƊUMI: An Fitar Da Jadawalin Shirye-shiryen Jana'izar Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari:

1-An ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu a Najeriya don makokin Marigayin 2-An kafa Kwamitin Manyan Jami'an gwamnati don tsara jan...


1-An ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu a Najeriya don makokin Marigayin

2-An kafa Kwamitin Manyan Jami'an gwamnati don tsara jana'izar girmamawa ga tsohon shugaba Buhari wanda sakataren gwamnatin tarayya Sen. George Akume ya jagoranta.

3-An dage taron Majalisar Zartarwa ta Kasa daga gobe zuwa juma'a don zaman makoki

4  An umarci mambobi 25 na Majalisar Zartarwar da su wuce Daura don halartar jana'izar zaman makoki na kwanaki uku

4-An ayyana kwanaki 7 na zaman makoki a ilahirin Najeriya tare da yin ƙasa-ƙasa da tutar kasar

5- Babbar tawaga karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa na can na kammala shirye-shiryen kawo gawar da iyalan mamacin gida

6- Za a yi takaitaccen faretin Sojoji a filin jirgin sama na jahar Katsina don tarbar gawar.

7- Za a yi Sallar Jana'iza da rufe gawar a Daura.

8 An bude shafin karbar ta'aziyya a dukkan ma'aikatun gwamnatin tarayya, da na hukumomi, da ilahirin ofisoshin jakadanci na Najeriya da ke kasashen waje.

9- Ana sa ran isowar gawar Katsina da karfe 12 na rana ranar Talata.

10- Za a yi Jana’iza a ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025.

10- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai karbi gawar tsohon shugaban kasa a Katsina tare da manyan baƙi

No comments