Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mutuwar Buhari: Ba Za Mu Yi Maraici A Siyasa Ba Matuƙar Tinubu Na Nan – Sanata Barau

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi watsi da raɗe-raɗin da ake cewa ‘ya’yan jam’iyyar APC, musamman ma masu bi...


Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi watsi da raɗe-raɗin da ake cewa ‘ya’yan jam’iyyar APC, musamman ma masu biyayya ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yanzu suna jin kamar sun zama marayu a siyasance.

Ya zanta da BBC Hausa jim kaɗan bayan kammala zama na musamman na Majalisar Zartarwa ta Tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Alhamis.

Ya kuma bayyana ra’ayin a matsayin ba gaskiya ba ne domin jam’iyya mai mulki a yanzu tana da babban jigo a wajen shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ganin cewa shi ne shugaban ƙasa na farko a jam'iyyar APC mai mulki, wasu na ganin kamar rashinsa zai jefa 'yan jam'iyyar cikin rashin uba a arewacin ƙasar. 

Sanata Barau ya yi fatali da hasashen yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu ne ubansu a yanzu.

''Ba haka ba ne, muna da babban shugaba, shugaba Bola Tinubu," inji shi. Ko lokacin da Allah ya sa Buhari ya zama shugaba ai tare suka yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Tinubu."

A cewar Barau Jibrin, ƙaddara ce ma ta sa Buhari ya riga Tinubu zama shugaban ƙasa a APC.

"Bola Tinubu ne ya zauna ya ƙirƙiro maganar kafa jam'iyyar APC, kuma ƙaddara ce ta sa Buhari ne zai fara shugabancin.

''Shugaban ƙasa na yanzu shi ya tsara komai, jam'iyyu huɗu suka dunƙule, da ACN da ANPP da CPC da kuma New PDP. Idan aka ce babu shugaba, wannan zance ne na adawa kuma babu gaskiya a cikinsa."

No comments