Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Gano Trump Na Fama Da Lalurar Jijiyoyin Jini Bayan Kumburin Ƙafa Da Hannu

Fadar shugaban Amurka ta White House ta sanar cewa Shugaban Donald Trump na fama da wata matsananciyar cutar jijiya. Hakan na zuwa ne bayan ...


Fadar shugaban Amurka ta White House ta sanar cewa Shugaban Donald Trump na fama da wata matsananciyar cutar jijiya. Hakan na zuwa ne bayan kwashe kwanaki ana raɗe-raɗi, bayan da hotuna suka nuna wani abu tamkar ƙujewa a fatar hannun shugaban.

Bayan samun wani kumburi a ƙafafunsa a kwanakin nan "An yi wa Trump binciken lafiya na ƙwaƙwaf" ciki har da gwajin jijiyoyin jini, kamar yadda sakatariyar ƴaɗa labarun fadar shugaban ƙasar, Karoline Leavitt ta bayyana.

Leavitt ta ce alamun da aka gani a fatar hannun Trump ya faru ne dalilin "koɗewar fata sanadiyyar shan hannu da mutane akai-akai" inda yake yawan shan ƙwayar maganin aspirin, wanda ta ce na daga cikin "matakan da aka saba amfani da su wajen kare cutukan hanyoyin jini".

Trump mai shekara 79 ya sha yin tutiya game da lafiyarsa, inda yakan bayyana kansa a matsayin "shugaban ƙasa mafi lafiya a tarihin Amurka".

Cutar da aka gano Trump na fama da ita, wato 'chronic venous insufficiency', wadda ke faruwa yawanci a lokacin da jijiyoyin da ke ƙafafu suka gaza harba jini zuwa zuciya, lamarin da ke sanyawa jini ya taru a ƙafa, kuma ya haifar da kumburi.

Jijiyoyi da bawul-bawul ɗin da ke cikinsu ne "suke tura jini sama zuwa wasu wuraren daga ƙafa" zuwa zuciya, in ji Dakta Meryl Logan, farfesar ilimin lafiya jijiyoyi a Jami'ar Texas da ke Austin.

Jinin da ke tasowa daga ƙafa suna yin sama na buƙatar harbawa, kuma wani lokaci abin na da wahala.

Leavitt ta ce "ba a ga wata alama ta cutar dunƙulewar jini ko kuma na jijiyoyin da ke ɗaukar jini daga jijiya zuwa sassan jiki ba", sannan kuma duk wasu gwaje-gwaje da aka gudanar ba su nuna cewa akwai hatsari sosai ba.

Wani bayani da likitan fadar shugaban Amurka Sean Barbella ya fitar ga manema labarai, ya ce yanayin "bai da hatsari kuma abu ne da aka saba gani", musamman a mutanen da suka zarce shekara 70 a duniya.

Wasu ƙarin gwaje-gwaje da aka gudanar sun nuna cewa "babu alamun matsalar zuciya, ko na ƙoda ko kuma wanda ya shafi jiki" a tattare da Trump", kamar yadda Barbella ya bayyana a bayanin da ya fitar wanda ke tabbatar da bayanin Leavitt.

No comments