Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Ɗage Ɗaukar Sababbin Jami'ai A Wasu hukumomin Tsaro

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta dakatar da aikin da take yi na ɗaukar sababbin jami'ai a hukumomi kamar Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa, Hu...


Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta dakatar da aikin da take yi na ɗaukar sababbin jami'ai a hukumomi kamar Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, Jami’an Tsaro na Sibil Difens da Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya.

A cikin wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan Yuli 16, 2025, Sakataren Hukumar Kula Gidajen Gayran Hali, Sibil Difens, Hukumar Kashe Gobara da Kula da Shige da Fice, Manjo Janar A.M. Jibril (mai ritaya), ya ce, za a sake buɗe manhajar a ranar Litinin, 21 ga Yuli, 2025.

“A wani bangare na ƙoƙarin inganta tsarinta, Cibiyar Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, Jami’an Tsaro na Sibil Difens da Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya (CDCFIB) ta sanar da cewa an dakatar da ɗaukar sabbin jami'ai na wani ɗan lokaci.

"Za a sake samun manhajar daga ranar Litinin, Yuli 21, 2025," inji Jibril.

Sakataren ya bayyana cewa dakatarwar za ta taimaka wajen tabbatar da tsarin zai iya sarrafa yawan masu neman shiga hukumomin yadda ya dace da kuma ba da damar ɗaukar su cikin tsari, gaskiya da adalci.

"Wannan ci gaban zai tabbatar da cewa manhajar ta intanet tana ɗaukar yawan jami'ai yayin da ke ba da garantin bin tsari na gaskiya da adalci.

Ya ƙara da cewa "Muna godiya da himma da sha'awar matasan Nijeriya na yi wa ƙasarsu hidima ta waxannan muhimman hukumomi kuma sun himmatu wajen tabbatar da tsarin ɗaukar jami'ai cikin gaskiya da adalci."

No comments