Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Fethullah: Hedikwatar Tsaro Ta Musanta Bullar Sabuwar Ƙungiyar Ta'addanci A Nijeriya

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta musanta iqirarin da jakadan Turkiyya a Nijeriya, Mehmet Poroy ya yi na cewa wata ƙungiyar ta'addanci na gu...


Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta musanta iqirarin da jakadan Turkiyya a Nijeriya, Mehmet Poroy ya yi na cewa wata ƙungiyar ta'addanci na gudanar da ayyukan ta a cikin yankunan Nijeriya a ƙarƙashin tsarin ilimi da kiwon lafiya.

A wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Markus Kangye ya fitar a ranar Alhamis, hedikwatar ta bayyana wannan iƙirari a matsayin "maganar ba a hukumance ba" kuma ba ta da tushe mai inganci, tana mai cewa Nijeriya a matsayinta na ƙasa mai cin gashin kanta, ba ta yarda da bayanan sirri na ƙasashen waje ba tare da tantancewar ta ba.

"Hedkwatar tsaro ba ta yarda iqirarin jakadan Turkiyya ba. kowa yana da 'yancin faɗin duk abin da yake so. Akwai 'yancin samun bayanai," inji Kangye.

"Nijeriya ƙasa ce mai cin gashin kanta wacce za ta iya yin tunani da aiki da kanta."

Ambasada Poroy da yake magana a wani taron da aka gudanar a Abuja ranar Talata da ta gabata na tunawa da ranar dimokuraɗiyya da hazin kan ƙasa ta Turkiyya, jakadan Poroy ya yi iƙirarin cewa mambobin ƙungiyar ta’adda ta Fethullah (FETO) na da ƙarfi a Nijeriya, musamman a fannonin ilimi da kiwon lafiya.

Poroy ya yi gargaɗin "Kasancewar irin wannan ƙungiya baraza ce ga kowace ƙasa da take gudanar da ayyukanta."

Turkiyya dai na ɗaukar 'yan ta'addar FETO a matsayin ƙungiyar 'yan ta'adda, inda ta ɗora mata alhakin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 15 ga watan Yulin 2016 kan shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Ana zargin ƙungiyar da alaƙa da marigayi malamin ƙasar Turkiyya Fethullah Gulen, wanda ya gudanar da harkokin makarantu da qungiyoyin agaji na duniya kafin rasuwarsa a shekarar 2024.

Yayin da Turkiyya ke ci gaba da muraushe cibiyoyi da ke da alaƙa da Gulen a duniya, qasashe da dama ciki har da Nijeriya ba su sanya qungiyar ta FETO a matsayin qungiyar ta'addanci ba, haka kuma ba su gabatar da hujjoji da ke tabbatar da irin wannan ilirarin a Nijeriya ba.

No comments