Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana cewa Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi wani gagarumin yunƙuri...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An bayyana cewa Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi wani gagarumin yunƙuri na biyan haƙƙoƙin ‘yan fansho da suka kammala aiki shekaru 35 da kuma waɗanda suka rasu a lokacin da suke aiki, wanda ke nuni da irinnl ci gaban da Gwamnan ya samar a shekarun sa biyu yana kulki.
Alhaji Habu Muhammad Fagge, shugaban amintattu na asusun fansho na jihar Kano ne ya bayyana hakan a tattaunawar sa da wakilin ku. Inda ya ce Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kawar da matsalolin 'yan fansho ta biya maƙudan kuɗaɗen 'yan fansho Naira biliyan 16.
Ya ƙara da cewa yanzu haka ma akwai Naira Biliyan Biyar da da suke a ƙasa da za a biya. Ya ce cikin shekaru biyun farko da ga rantsar da shi wanda ya kawo ɗauki ga ɗaruruwan ‘yan fansho da iyalansu.
Alhaji Habibu ya ce, a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, jihar Kano ta samu gagarumin sauyi a harkokin mulki da samar da ayyuka da kuma jagoranci. Jihar ta aiwatar da aikace-aikace da inganta ababen more rayuwa, farfad)ɗo da ilimi, inganta harkokin kiwon lafiya, da tsare-tsare na ƙarfafa matasa, wanda hakan ya sa yake samun kyakkyawan shaidar yabo a kasar baki daya.
"Fitattun nasarori sun haɗa da ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi da sanya kaso mai yawa a kasafin kuɗin 2024 da na 2025 ga ilimi da ake ta aiwatar da ayyuka da ke inganta tsarin ilimi. An kuma habaka tsarin kiwon lafiya da inganta Asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko."
Alhaji Habu Muhammad Fagge ya danganta waɗannan nasarorin da irin yadda Gwamnan ya jajirce wajen kyautata rayuwar al’ummar Kano da kuma dogon hangen nesansa na samar da ci gaba mai dorewa.
Shugaban hukumar asusun amintattu na fansho na jihar Kano ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da yi wa Gwamnan da dukkan muƙarraban Gwamnatinsa jagora wajen ci gaba da hidimta wa bunƙasa ci gaban al'ummar Jihar Kano.
No comments