Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hadarin Ambaliya: Sanata Wamakko Ya Buƙaci Mutane Su Guji Zaman Kusa da Koguna

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kira ga mazauna jihar Sakkwato da su dauki matakan kariya tun kafin ambaliya ta afku, kamar yadda Huk...


Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kira ga mazauna jihar Sakkwato da su dauki matakan kariya tun kafin ambaliya ta afku, kamar yadda Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMET) ta yi hasashe.

Sanatan ya bayyana hakan ne bayan kammala sallar Idi a gidansa da ke Gawon Nama, inda ya karbi bakuncin manyan baki da kuma sauran al’umma.

NiMET ta yi gargadi a cikin Hasashen Yanayin Shekara ta 2025 cewa za a fuskanci ruwan sama mai yawa da kuma yiwuwar ambaliya a wasu jihohi, ciki har da Sakkwato. Hukumar ta kuma bayyana damuwa kan yaduwar cututtukan da ke da nasaba da ruwa kamar kwalera, musamman a wuraren da ke da matsalolin tsafta.

A cewar NiMET, jihohin Arewa da suka hada da Sakkwato, Katsina, Zamfara, Kano, Jigawa, Yobe da Borno za su fuskanci ruwan sama a tsawon kwanaki 110 zuwa 150 a bana.

Sanata Wamakko, wanda ya taba fuskantar mummunar ambaliya a shekarar 2010 lokacin da yake Gwamnan Jihar Sakkwato, ya bayyana muhimmancin shiryawa tun da wuri. Ya bukaci jama’a da ke zaune kusa da koguna da su matsa daga wuraren, ko su tabbatar da cewa hanyoyin ruwa a bude suke domin ruwa ya rika gudana ba tare da cikas ba.

“Ya kamata mu dauki wannan lamari da muhimmanci. Na shaida irin barnar da ambaliya ke yi. Kowa ya kula da hasashen NiMET ya kuma dauki matakin da ya dace domin kare rayuka da dukiyoyi,” in ji Wamakko.

Sanatan ya kuma gode wa al’umma bisa addu’o’insu da goyon baya da suke bai wa gwamnati. A wajen taron, Malam Nafi’u Malami Dan Haja ya jagoranci addu’a ta musamman domin zaman lafiya da daurewar tsaro.

Taron ya samu halartar fitattun mutane da suka hada da Ministan Kwadago da Ayyukan Yi, Muhammad Maigari Dingyadi; karamin Ministan Ayyuka, Barista Bello Muhammad Goronyo; da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Chuso Abdullahi Dattijo.

Wannan kira na Sanata Wamakko na zuwa ne a wani lokaci mai matukar muhimmanci a yayin da al’ummomi ke shirin fuskantar damina da ake sa ran za ta kawo kalubale ga ababen more rayuwa da daukar matakan gaggawa a fadin kasar.

No comments