Daga Ibrahim Muhammad, Kano Gidauniyar Hausa da haɗin kan Hausawan Duniya "Charity" ƙarƙashin jagorancin shugabanta na Duniya Da...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Gidauniyar Hausa da haɗin kan Hausawan Duniya "Charity" ƙarƙashin jagorancin shugabanta na Duniya Dakta Muhammad Sa'id ta gudanar da taron bayar da muƙamai da shaida ga wasu daga mambobinsu.
Taron da aka gudanar a Kano ya sami halartar ɗimbin mambobin Gidauniyar daga cikin da wajen ƙasar nan. A yayin taron, shugaban Gidauniyar ya bayyana cewa waɗannan naɗe-naɗe da aka yi zai ƙara bunƙasa cigabansu.
Daga nan ya yi nuni da cewa Nijeriya ita ce cibiyar wannan ƙungiya, shi ya sa suka zaƙulo waɗannan jajirtattun mutane suka ƙara sanya su a cikin ƙunshi na shugabancin Gidauniyar.
Dakta Muhammad Sa'id ya yi kira ga al'ummar Hausawa a faɗin Duniya akan su haɗa kai domin kawar da matsala da ake samu na rashin haɗin kai a tsakanin Hausawa shi ya sa suke wannan ƙoƙari ko'ina a Duniya game da samun wannan haɗin kai.
Dakta Muhammad Said ya ce mutane biyar da aka baiwa shaidar mukaman akwai na matsayin koodinata na Gidauniyar na Duniya da kuma Tauraruwa ta Duniya da kuma Sakataren janar na Gidauniyar na Duniya da shugaban matasa na kasa.
Ya ce ana yin duba da dacewa da cancanta ne kafin a bayar da irin wannan matsayin sun bincika wadanda suka sami muƙaman sun cancanta da matsayin, domin suna da kyakkyawan shaida a wajen jama'a.
Dakta Muhammad Sa'id ya ce Gidauniyar yanzu ta soma karɓuwa a kasar nan, ba kamar sauran kasashe da suka kafa reshen su ba da suka sami karɓuwa sosai, a nan Nijeriya akwai yan kalubale da ake fuskanta saboda akwai wasu kananan kungiyoyi da suke kallon wannan Gidauniyar ta Hausa da hadin kan Hausawan Duniya "charity "barazana ce a garesu wanda kuma ba haka bane, suna gudanar da tafiyar da ita ne bisa sahalewar doka.
Shi ma Koodinata na Gidauniyar na Duniya Alhaji Rabiu Muhammad Gumel ya ce duk lokacin da za ka yi irin wannan Gidauniya da ta shafi duniya sai ka zauna ka ga su waye ma za su kasance a ciki ,don sai ka sami jajirtattun mutane da zasu tafiyar da ita don haka akwai matakai da akan bi don tantance mambobinta domin samun sahihanci da ingantattun mambobi jajirtattu da shugabanni ake sawa.
Ya ce a matsayinsa na koodinata na Gidauniyar na Duniya a halin yanzu da suke da wakilai a kasashen duniya 47 mafi yawan Wakilansu da suke kasashen Duniya mutane ne Hausawa yan asalin kasashen wasu kasuwanci ne ya kai su da iyalansu suke zaune, sun zama yan kasa suna da katin kasa da kuma mafi yawa wasu ma a can aka haife su.
Ya yi kira ga mambobin Gidauniyar su sani cewa wannan aiki ne suka dauko, wani abu ne na fafutuka domin irin wannan shi suka rasa a baya, yanzu lokaci yayi da za a zage damtse ,yanzu an sami wata kafa ta samun wani jigo da za su rike akai inda ba a tunanin akai
Alhaji Rabiu Muhammad Adam Gumel
Jakadan Lautai koodinata na Gidauniyar Hausa da hadin kan Hausawan na Duniya ya ja hankalin masu kokarin su shigo tafiyar Gidauniyar su sani ana maraba da kowa, domin ta kowane bahaushe ce da yake Duniya domin a hadu a gudu tare a tsira tare kuma tasirinta Bahaushe bai taba samun wata Gidauniya irin wannan ba da ta tsaya ta kalli bahaushe da kuma ina yake so yaje , wannan tasa suna da tunanin harshen Hausa zai sami kujera ma nan gaba a majalisar Dinkin Duniya wannan shine burinsu.
A yayin jawabinsa shima shugaban Gidauniyar Hausa da hadin kan Hausawan Duniya reshen Nijeriya.Alhaji Shitu Adam Bargaja shugaban Kungiyar Sakkwatawa da kabawa da Zamfarawa mazauna jihohin Kano da Jigawa ya bayyana farin cikinsa da taron da kuma kira ga mambobin Gidauniyar su dage wajen hada kan al'ummar Hausawa a duk inda suke domin tabbatar da kima da wanzuwar al'adunmu.

No comments