Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Bola Ahmed Tinubu Na Aiki Tsawon Sa’o’i 18 a Kowace Rana Don Inganta Ci Gaban Nijeriya

A cikin wani rubutu mai ƙayatarwa mai taken Rana Ɗaya Tare da Shugaba Tinubu wanda Sam Omatseye ya wallafa a jaridar The Nation a ranar 26 g...

A cikin wani rubutu mai ƙayatarwa mai taken Rana Ɗaya Tare da Shugaba Tinubu wanda Sam Omatseye ya wallafa a jaridar The Nation a ranar 26 ga Mayu 2025 an bai wa ‘yan Nijeriya damar ganin yadda rayuwar yau da kullum ta ke ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ke ɗaukar shugabanci a matsayin aiki na cikakken lokaci ba tare da hutawa ba.

Tun da sassafe Shugaba Tinubu kan fara da karanta takardun sirri na gwamnati da bayanan leƙen asiri tare da tarurrukan shawarwari da mashawartansa Wannan tsarin na nuna yadda ya ke da kishin ƙasa da kuma jajircewa wajen tabbatar da cewa kowane mataki da gwamnati ke ɗauka yana da tushe mai karfi.

Yayin da ake tattauna batun tsaro musamman a Jihar Filato Shugaba Tinubu ya bayyana cikakkun matakai da shirye-shirye don kawo zaman lafiya mai ɗorewa Ba wai kawai magana ba ce ta siyasa amma dai shiri ne mai zurfi da nufin magance matsalolin tsaro ta hanyar aikace aikace

Haka kuma ya bayyana wani babban jari na Dala Biliyan 2.5 daga kasar Brazil domin inganta harkar noma da kiwo a Nijeriya Shugaban ya yi nufin shigo da taraktoci 2000 tare da kafa tsarin bin diddigin dabbobi ta hanyar fasaha domin magance rikice rikicen manoma da makiyaya da kuma bunkasa samar da abinci

A taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya Shugaba Tinubu ya nuna cewa yana so a rage dogon tsarin aiki domin a fi mayar da hankali kan batutuwan da za su kawo sauyi kai tsaye ga rayuwar ‘yan kasa Ya nuna jagoranci mai cike da hangen nesa da fahimta inda ya karfafa gwiwar ministoci su fito da tsare tsare masu amfani kai tsaye ga al’umma

Daga farko har zuwa ƙarshen rana Shugaba Tinubu na cikin aiki yana sa ido kan duk wata muhimmiya da ke shafar mulki Ba ya barin komai ya wuce ba tare da sa hannunsa kai tsaye ba Tsarin mulkinsa na nuna shugaba mai aiki tukuru wanda ke tafiyar da kasa da hangen nesa da kuma jajircewar kawo sauyi mai ma’ana

Rahoton Sam Omatseye ya bayyana Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaba mai aiki daga safiya har dare ba tare da gajiyawa ba Mulkinsa yana misalta shugabanci mai kishi da tsari da kuma jajircewar ganin Najeriya ta tsaya kan turbar ci gaba da bunkasuwa.
 

No comments