Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

SHEKARU BIYU A KARAGAR MULKI: Buhari Ya Taya Shugaba Tinubu Murna

Tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya taya shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekaru biyu a kan mulki, tare da cewa kamar ...


Tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya taya shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekaru biyu a kan mulki, tare da cewa kamar yadda jam’iyya da gwamnati ke murna, ya kuma kamata 'yan ƙasa su tuna cewa shugabanci tafiya ce marar iyaka.

Buhari ya kuma ya kira da a ci gaba da mara wa gwamnatin APC baya domin sauyi ba ya samuwa nan take, dole sai sannu a hankali.

Ya kuma yaba da irin ƙoƙarin da gwamnatin ke yi wajen magance matsalolin talauci da tsadar rayuwa, sannan kuma ya ƙara da cewa ka da a bar alhakin shawo kan matsalar kacokam a kan gwamnati, dan haka ya zama wajibi kamfanoni masu zaman kansu da sauran ƴan ƙasa su ma su ba da tasu gudunmawar ta duk hanyar da za su iya.

Ya kuma ƙara da kira ga ƴan Najeriya da su ƙarfafa imaninsu kan samun kykkyawar gobe a ƙasar nan.
 

No comments