Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Babbar Manufar mu, Ita Ce Cusa Ɗa'a Da Kishin Ƙasa Ga 'Yan Arewa - Shugaban AIRLIN

Wata qungiyar mai zaman kanta da ke wayar da kan al'ummar Arewacin Nijeriya kan muhimmancin yin zave, cusa xa'a, nuna kishin qasa da...


Wata qungiyar mai zaman kanta da ke wayar da kan al'ummar Arewacin Nijeriya kan muhimmancin yin zave, cusa xa'a, nuna kishin qasa da kyautata tarbiyya mai suna 'Advocacy for Integrity and Rule of Law Initiative' (AIRLIN) ta yi kira ga ’yan Nijeriya, musamman mazauna yankin Arewa da su shiga cikin harkokin zave ta hanyar amfani da ’yancin da tsarin mulki ya ba su da kuma zaven shugabanni nagari.

Shugaban qungiyar na qasa, Alhaji Muhammad Ibrahim Gamawa ne ya yi wannan kiran a yayin bikin qaddamar da shugabannin jiha da qananan hukumomin Jihar Kaduna a Arewa House, ranar Talata.

Gamawa ya jaddada cewa, manufar qungiyar tasu ita ce a bai wa ’yan Nijeriya shawarar su kasance masu bin doka da oda, da mutunta juna ba tare da la’akari da bambancin addini da al’adu ba, yana mai cewa, kare martaba Nijeriya aiki ne da ya rataya a wuyan ’yan qasa, a ciki da wajen Nijeriya.

“Don haka ne ma muka zo nan domin aaddamar da xaya daga cikin ofisoshi 15 da muke da su a jihohin Arewa 19, domin burinmu shi ne mu mamaye dukkan jihohin Arewa, mun zo ne domin mu yi kira ga ‘yan qasa su zo su kaxa auri’a a cibiyar da za su zavi shugabanni nagari.

“Idan za a iya tunawa a zaven da ya gabata, kashi 42 cikin 100 na masu kaxa quri’a ne kawai suka halarci wurarren zave, 68 kuma ba su halarta ba wanda hakan ba shi da kyau ga qasar nan, don haka dole ne mu fito mu san waxanda suka kasa zave, mu fahimtar da su su zavi shugabanni da suka dace.

A wani vangare na manufofinsu na qara yawan masu kaxa quri’a, Alhaji Gamawa ya bayyana cewa, qungiyar mai zaman kanta za ta taimaka wa ‘yan qasa wajen karvar katin zave, “Lokacin da INEC ta buxe dandalin rajistar katin zave, za mu taimaka musu wajen karvar katin zave domin su bada gudunmawa a zave da kuma amfani da ’yancinsu.

Gamawa ya kuma yi magana kan muhimmancin samun katin shaidar zama xan qasa, inda ya ce, yayin da tsaro ya yi qaranci, abu ne mai sauqi a laqa wa xan Nijeriyar ba shi da katin xan qasa sharrin zama baqo ko xan mamaya ko kuma sanya shi cikin masu garkuwa da mutane.

“Rashin katin shaidar zama xan qasa babbar matsala ce ga ’yan Nijeriya musamman waxanda ke zuwa yankin Kudancin qasar nan.

“Amotekun ko wasu qungiyoyin al’adu ne za su tare su, za a tattara su a ce su bayyana kansu da kuma inda suka fito, wasu ma suna zargin su ba ’yan Nijeriya ba ne.

"Wasu za su ce 'yan Kaduna ne amma ina katin shaida? Babu wata shaida ko da ta lasisin tuqi ce."

Ya kuma bayyana cewa, qungiyarsa na shirin gudanar da wani taro na kwana xaya domin karvar baquncin Malamai aqalla 200 a qaramar hukumar Gamawa waxanda za su zo a wayar da kan jama’a game da gina qasa da haqqoqin ‘yan qasa da ayyukansu sannan kuma su wayar da kan xalibai da ke qarqashinsu.

A nasa jawabin, shugaban AIRLIN na Jihar Kaduna Alhaji Musa Muhammed ya ce, qungiyar ta duqufa wajen ganin ta kawo sauyi mai kyau da zai dawo da martaba da mutunta ‘yan Nijeriya.

Ya qara da cewa, AIRLIN gida ce ga kowa da kowa musamman waxanda suka yi imanin cewa akwai buqatar a sake farfaxo al'amuran da suka rushe a Nijeriya.

Taron dai ya samu halartar dukkan shugabannin qungiyar na jiha da na qananan hukumomin jihar, tare da 'yan rakiyar shugaban na qasa da suka taho daga Abuja.

No comments