Daga Ibrahim Muhammad Ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Nasarawa Hon. Hassan Shehu Hussain ɗaya ne daga 'y...
Daga Ibrahim Muhammad
Ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Nasarawa Hon. Hassan Shehu Hussain ɗaya ne daga 'yan majalisar da ya ke samun kyakkyawan shaida na gudanar da ayyuka daban-daban a mazabarsa.
Al'ummar Ƙaramar Hukumar Nasarawa, hatta 'yan adawa suna da kyakkyawan shaida akansa na gudanar da ayyuka da yake yi musu a fannoni daban -daban da babu mai musun haka duk da cewa wannan shi ne zuwansa majalisar tarayya na farko.
Sannanen abu ne a kundin tsarin mulkin Nijeriya babban aikin ɗan majalisa a kowane mataki shi ne ya kai ƙudiri akan abin da ya shafi ci gaban al'umma, a yi duba akan muhimmancinsa da amfaninsa ga ci gaba, a yi masa karatu a yi doka akai.
Ko a 'yan kwanakin nan ya gabatar da ƙudirin na neman Gwamnatin tarayya ta kawo ɗaukin gaggawa ga masana'antun Kano ta tallafa musu da inganta harkar wutar lantarki.
Sannan akwai ƙudirin da ya kai domin bunƙasa Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da kuma samar da cibiyar kula cutukan zuciya a Asibitin.
Kai irin wannan ƙudiri ba kowane ɗan majalisa ne ke iya miƙewa ya yi ba, hatta 'yan majalisu da suka jima suna zuwa majalisar wasu ba su taba wani motsi don gabatar da wani ƙuduri ba.
Sannan kuma, sanannen abu ne ga al',ummar jihar Kano ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Nasarawa Hon. Hassan Shehu Husaini yana daga cikin waɗanda suka ciri tuta wajen kai ƙudiri farfajiyar majalisar tarayya akan abin da ya shafi al'ummarsa da ci gaban jihar Kano.
Zuwan sa majalisa don wakiltar alummar Ƙaramar Hukumar Nasarawa ya shigar da ƙudurori da dama da suka tsallake karatu har suka tabbata.
A bangaren ayyuka kuwa irin gudunmawar da yake bayarwa a bangaren Ilimi ya haɗa da sama wa matasa Maza da Mata gurbi a manyan makarantu da biya musu kuɗaɗen makarantun a kwalejin ilimi na sa'adatu Abubakar Rimi da Kano polytechnic da collage of art and remedial studies, School of health and technology, inda ɗalibai 600 suka ci gajiya.
Ya kuma biya kuɗin jarabawar WAEC, NECO, JAMB na mutun 1800. Sannan ya ɗauki nauyin karatun marayu 150 tun daga makarantar renon ' nursery' har zuwa makarantar gaba da sakandire..
Haka fannin samar da Ruwan sha ya gina Rijiiyoyin burtatse guda 30 a mazabun karamar hukumar Nasarawa 11. Ya samar da tituna
masu tsawon kilomita Biyu-biyu a mazabun Gama da Tudun Wada. Haka a mazabar Gawuna,
da Tudun Murtala da mazabar Hotoran Kudu ya samar da tituna masu tsawon kilomita daya.
A bangaren inganta samar da wutar lantarki ya samar tiransifoma na wuta mai karfin KW 500 a mazabar Gwagwarwa da mazabar Hotoran alArewa da mazabar Hotoron Kudu.
A bangaren gine -gine ya gina rukunin ajujuwa 3 a makarantar Firamare ta Ladanai. A mazabar Hotoron Arewa kuma ya samar da gini mai ajujuwa Biyu a makarantar community school a Unguwar Tishama, Hotoron Arewa ya gina ajujuwa Biyu a makarantar sakandire da ke Dakata.
A bangaren inganta lafiya ya samar da ginin Asibitin sha ka tafi "Clinic hospital" da kayan aiki a Unguwar Yandodo Hotoran Arewa. Sannan ya samar da fitilu masu amfani da hasken Rana a dukkanin mazabu 11 na Ƙaramar Hukumar Nasarawa.
Hon. Hassan Shehu Husaini a ƙarƙashin wannan wakilcin nasa ya sama wa matasa aikin yi a mataki na Gwamnatin jiha da na tarayya kimanin mutum 20.
Sannan yana bayar da tallafi domin Gina rayuwar al'umma a bangarori da dama da matasa maza da mata da iyaye da dama suka anfana. Sannan a cikin watan azumin da na sallah ya tallafa wa al umma da abubuwan more rayuwa ta fannoni daban daban domin gina rayuwar su.
Duk wadannan ayyuka da dan majalisar tarayya na Nasarawa Hon. Hassan Shehu Husaini yake sauke nauyi ne na al'ummar da suka zabe shi ,wanda a ma'auni na adalci yana yin abin da ya dace da ya shafi ci gaban al'ummar sa.
Wasu yan siyasa sun ce Idan aka samu wasu na kalubalantar sa a iya cewa suna yine kawai saboda wani abu da ya haɗa su da shi akan kansu, amma ba don gazawa a wajen a sauke nauyin wakilci da al'ummar ƙaramar hukumar Nasarawa suka dora masa ba a majalisar tarayya.
Muhimmin aikinsa da doka ta tanada masa shine kai kudiri, yin ayyukan alummar sa kuma yana yi suma masu sukar sa, basa zarginsa da gazawa a wannan bangaren.
Sai da Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya jinjina wa kokarin da ɗan majalisar yake a wani taro na buɗe hanyoyi da ɗan majalisar ya yi har ya yi jan hankali ga sauran 'yan majalisa su yi koyi da shi.
Ibrahim Muhammad ya rubuto mana wannan ne daga Kano.
No comments