By Hussaini Yero, Gusau Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Lawal, ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su wayar da kan al’umma k...
By Hussaini Yero, Gusau
Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Lawal, ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su wayar da kan al’umma kan cutar ƙyanda domin su rungumi allurar rigakafin cutar don kare lafiyar yara a faɗin jihar.
Uwargidan gwaman ta yi wannan kiran ne a lokacin da ta ke ƙaddamar da gangamin wayar da kan jama’a kan cutar ƙyanda a Gusau babban birnin Jihar Zamfara.
Ta ce, matakin farko na rigakafin za a yi wa yara ‘yan tsakanin watanni zuwa shekara 15, kuma rigakafin da za a yi zai kai watanni 9 zuwa 5.
Daga nan Huriyya Dauda ta gode wa ƙungiyoyin kiwon lafiya a bisa tallafin da suke bayarwa wajen magance duk wani ƙalubalen kiwon lafiya da ya addabi jihar.
A nasa Jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yi kira ga Sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai don ganin yara a yankunansu sun samu rigakafin cutar don kare su daga cututtuka masu kashe yara.
Shi kuwa, a nasa jawabin, mai ba da shawara kan harkokin yara na sashen kula da lafiyar ƙananan yara na tarayya dake Gusau, Dokta Ibrahim Hano ya bayyana cutar ƙyanda da rubella a matsayin cututtuka masu kashe yara ƙanana.
Hano ya ce, cutar ƙyanda da rubella suna haifar da makanta, matsalar ƙwaƙwalwa da ciwon zuciya a tsakanin yara idan ba a yi musu rigakafi ba.
Shi ma da yake nasa jawabin, Sarkin Anka, kuma shugaban majalisar Sarakunan jihar, Alhaji Attahiru Ahmad, ya yaba wa gwamnatin jihar da ƙungiyoyin kiwon lafiya bisa jajircewarsu wajen samar da kiwon lafiya a Zamfara.
Ya yi alƙawarin bayar da cikakken goyon bayansu da wayar da kan al’ummarsu don su kai ‘ya’yansu rigakafin waɗannan cututtuka masu kisa.
No comments