Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

MA’AIKATAN JAMI’O’I ZA SU DARA: Gwamnati Ta Sakar Masu Naira Biliyan 50

li A halin da ake ciki dai gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta kammala shirye-shirye don ƙara kyautata rayuwar ma'aikatan kasar nan, ...

li
A halin da ake ciki dai gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta kammala shirye-shirye don ƙara kyautata rayuwar ma'aikatan kasar nan, inda ta saki Naira biliyan 50 ga Jami’o’in gwamnatin tarayya.

Ministan harkokin Ilimi, Dakta Maruf Olatunji Alausa ne ya bayyana haka, inda ya ce, wannan mataki yana daga cikin cikar alƙawuran shugaba Tinubu wajen inganta harkar ilimi da tabbatar da zaman lafiya a cibiyoyin ilimi.

Ministan ya bayyana cewa, “Wannan ba kawai biyan kuɗi ba ne, alama ce ta yadda shugaban ƙasa ke mutunta rawar da Malamai da ma’aikatan Jami’o’i ke takawa wajen gina makomar matasan Nijeriya.”

Ya ƙara da bayyana godiyar gwamnatin tarayya ga ƙungiyoyin Malamai da ma’aikata bisa haɗin kai da fahimtar juna da suka nuna, wanda hakan ya kawo daɗaɗɗen zaman lafiya a jami’o’in.

Shugaba Tinubu ya na da ra'ayin cewa, “Matasa su ne zuciyar ƙasar nan. Goben su na da matuƙar amfani gare ni da gwamnati na. Tabbatar da matasan mu sun sami karatu abu ne mai muhimmaci. Na ƙuduri aniyar kawo ƙarshen yajin aiki a Jami’o’in ƙasar nan gaba ɗaya.”

Wannan mataki na cikin shirin “Renewed Hope Agenda” da ke nuna yadda gwamnatin ke ɗaukar harkar ilimi da muhimmanci domin ciyar da Nijeriya gaba.

No comments