Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Iran Ta Yi Tayin Raba Fasaharta Da Ƙasashen Afirka A Fannin Tsaro

Shugaban Ƙasar Iran, Massoud Pezeshkian ya bayyana cewa yana da fatan ƙara ƙarfafa dangantaka da ƙasashen Afirka. Ya shaida wa taron tattali...


Shugaban Ƙasar Iran, Massoud Pezeshkian ya bayyana cewa yana da fatan ƙara ƙarfafa dangantaka da ƙasashen Afirka.

Ya shaida wa taron tattalin arziki tsakanin Iran da ƙasashen Afrika a birnin Tehran cewa ƙasarsa tana da shirin bayar da ƙwarewarta a fannin tsaro da sauran fannoni kamar yadda ofishinsa ya bayyana.

Shugaban ya zargi wasu ƙasashe da ba a bayyana ba, waɗanda ake hasashen ƙasashen Yamma ne da aikata ayyukan tarzoma a sauran ƙasashe da kuma aikata laifuka a kan ɗan'adam.

"Maimakon shuka ƙiyayya da gaba, ya kamata mu jajirce wajen sada zumunci da ‘yan uwantaka da ƙauna, da kasuwanci, da kuma girmama haƙƙin juna," inji shi.

Ana gudanar da taron ne a Tehran daga 27 zuwa 29 ga watan Afrilu, sannan za a ci gaba da taron a Isfahan daga 30 ga watan Afrilu zuwa 1 ga watan Mayu.

Rahoton kafar yaɗa labarai ta ISNA ya bayyana cewa wadanda suka halarci taron sun hada da ‘yankasuwa 700 daga kasashen Afirka 38, da ministoci fiye da 50 da shugabannin majalisar ƴankasuwa daga ƙasashe 29 na Afirka.

Jaridar gwamnatin Zimbabwe, Sunday Mail, ta ruwaito jiya cewa taron yana daga cikin dabarun Iran na zurfafa dangantakar tattalin arziki da ƙasashen Afirka da kuma ƙara girman cinikayya, wadda a yanzu ta kai kusan dala biliyan 1.4 a shekara.

No comments