Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Babu Rabuwar Kai A Majalisar Dokokin Jihar Zamfara -Shugaban Majalisar

Daga Hussaini Yero, Gusau Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon Bilyaminu Moriki, ya tabbatar da cewa, Majalisar Dokokin na nan dara...

Daga Hussaini Yero, Gusau

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon Bilyaminu Moriki, ya tabbatar da cewa, Majalisar Dokokin na nan daram, ba ta rabu gida biyu ba, ya kuma yi watsi da zaman majalisar da wasu ‘yan majalisar 10 da aka dakatar suka kafa, inda ya ce majalisar ta saba wa doka kuma ba ta da tushe.

Da yake jawabi ga manema labarai a ofishinsa a jiya  Alhamis, Hon. Moriki ya jaddada cewa Majalisar Dokokin jihar Æ™arÆ™ashin jagorancinsa ita ce kaÉ—ai halastacciyar Majalisar da aka ba da izinin gudanar da ayyukan majalisa a jihar Zamfara.

 “A jiya an samu rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani game da wani zaman majalisar guda É—aya da ake yi a jihar, bari in bayyana cewa jihar Zamfara tana da halastacciyar majalisar wakilai É—aya tilo, duk wani zaman majalisa dole ne ya kasance a cikin harabar majalisar da ke Gusau.” In ji shi.

Hon.Moriki ya kuma yi watsi da matakin da ‘yan majalisar su 10 da aka dakatar, inda ya ce, “WaÉ—anda suka shirya taron da ake kira lokacinsu ne kawai, musamman ganin yadda shari’ar su ke gaban kotu, dan haka ba zan yi Æ™arin bayani ba har sai kotu ta yanke hukuncin,” inji shi.

A ranar Larabar da ta gabata rahoton bullar Majalisar Dokokin da 'yan majalisar guda 10 suka kafa, ya bayyana waÉ—anda shugabannin Majalisar Dokokin jihar a yanzu suka dakatar da su.

Sabuwar Majalisar, Æ™arÆ™ashin Shugaban ta, Hon. Bashir Gumi ta balle a Gusau a ranar Larabar da ta gabata, ta kuma ba Gwamna Dauda Lawal wa’adin wata É—aya, inda suka buÆ™aci da a É—auki matakin gaggawa kan tabarbarewar tsaro a jihar ko kuma a gurfanar da su a gaban Æ™uliya.
 

No comments