Sabon rahoton Bankin Duniya game da Nahiyar Afirka ya nuna cewa za a samun ƙarin adadin mutanen da za su talauce a Nijeriya da kaso 3.6 nan ...
Sabon rahoton Bankin Duniya game da Nahiyar Afirka ya nuna cewa za a samun ƙarin adadin mutanen da za su talauce a Nijeriya da kaso 3.6 nan da shekarar 2027.
Rahoton, wanda aka fitar a yayin zaman Asusun bada Tallafi na Duniya (IMF) da Bankin a Birnin Washington DC, ya nuna cewa, Nijeriya ƙasa ce da ta dogara da albarkatun mai da tattali mai fuskantar barazana gami da ƙalubale a shugabanci.
Ya bayyana cewa, hakan ka iya haifar da koma-baya ga ƙoƙarin rage matakin talauci acikin al’ummar ƙasar.
Babban Bankin Duniya ya ce, kaso 19 da Nijeriya ke da shi ya nuna cewa kimanin mutane miliyan 106 ne suke fama da matsanancin talauci a Nahiyar, kuma ya ke wakiltar kaso 15 na adadin talakawan duniya.
Sauran ƙasashen da suke fama da matsanancin talauci sun haɗa da Demokraɗiyyar Jamhuriyar Congo da kaso 14, Ethiopia mai kaso 9 da kuma Sudan da kaso 6.
Lamarin da ya nuna Nijeriya da sauran ƙasashe ukun sun wakilci rabin ƙasashen da suka fi talauci a Afirka a yankuna masu Sahara.
Masana na ganin za a iya samar da mafita ga hakan wajen fifita ayyukan inganta harkokin tattalin arziƙi gami da ƙarfafa harkokin kula da dukiyar ƙasa.
No comments