Daga Hussain Yero, Funtuwa Zaɓen Kananan Hukumomi a Jihar Katsina, Jamiyyar APC ta Kaddamar da "yan takarar Kamsiloli da Shugaban Ƙa...
Daga Hussain Yero, Funtuwa
Zaɓen Kananan Hukumomi a Jihar Katsina, Jamiyyar APC ta Kaddamar da "yan takarar Kamsiloli da Shugaban Ƙaramar Hukuma da mataimakin sa, a Maskan cikin Ƙaramar Hukumar Funtuwa Jihar Katsina.
Masu ruwa da tsaki na Jam'iyyar APC da masu muƙaman Siyasa ne suka Jagoranci ƙaddamar da Kamfen ɗin a garin na Maska.
Da ya ke bayani, Kwamishinan lafiya na jihar Katsina Hon Musa Adamu Funtua, ya bayyana cewa, sun zo tushen Funtuwa, watau Maska dan neman albarka na Ƙaddamar da yaƙin Neman nasarar zaɓen Ƙananan Hukumomi da Hukumar Zaɓen Mai zaman kanta ta Jihar Katsina za ta gudanar a ranar 15/02/2025 domin sake zaɓen 'yan takarar mu na Jamiyyar APC baki ɗaya".
Hon Musa Adamu ya kuma tabbatar da cewa, zaɓukan da suka gabata da al'ummar jihar Katsina suka zaɓi Jamiyyar APC sun tabbatar ba su yi zaɓen tumun dare ba, domin sun ga ayyukan da mai girma gwamnan Katsina Malam Dikko Radda ya ke zubawa a faɗin Jihar ta Katsina. Kuma an ɗauki ma'aikata da kuma turo 'yan jahar Katsina ƙaro karatun a jami'oin wajen ƙasar nan, musammam ma'aikatan lafiya don kula da lafiyar al'ummar Jihar Katsina.
"A kan haka ne muke miƙa ƙoƙon barar mu ga al'ummar Karamar Hukumar Funtuwa da na jihar Katsina baki ɗaya da su sake zaɓen 'yan takarar mu don ci gaba da ayyukan more rayuwa ga al'ummar.
Da ya ke gabatar da 'yan takarar, Jigon A Jamiyyar APC, Hon. Shamsu Sule ya ƙalubalanci wani jigo a Jam'iyyar adawa, inda ya bayyana cewa, sun shirya tsaf wajen fafatawa da duk wani mai ja da gwamnatin Dikko Radda a faɗin Jihar Katsina, kowa wane ne. "Kuma Ina kira gare shi da ya ja bakin sa ya yi shiru, idan ba haka ba, lallai za mu fasa ƙwai al'ummar Jihar Katsina su tabbatar da cewa makiyinsu ba masoyin su ba.
Dan majalisa tarayya, mai wakiltar Kananan Hukumomin Funtua-Dandume a Majalisar Wakilai, Hon Abubakar Gardi ya baje kolin ayyukan da ya yi ma al'ummar mazaɓar sa. A kan haka ne shi ma ya ke roƙon ƙuri'ar su ga 'yan takarar su na Shuganin Kananan Hukumomi da Kansiloli a zaɓen mai zuwa.
A nasa Jawabin, Dan Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Hon Abubakar Total ya bayyana cewa duk 'yan takarar su babu bara-gurbi. Don haka duk Wanda aka zaɓa lailai za su yi abin da ya kamata na ci gaban Karamar Hukumar Funtuwa.
Shugaban Hukumar Amsar Haraji ta jihar Katsina, Alhaji Aminu Isyaku ya bayyana cewa, ayyukan da gwamna Radda ke yi a Karamar Hukumar Funtuwa da Jihar Katsina baki daya na ci gaban al'umma ya kamata muduba mu zaɓi 'yan takarar Jam'iyyar gwamna Radda ta APC a zaɓen Kananan Hukumomi da za a gudanar a ranar 15/2/2025 .dan nuna godiya ga reshi .
Shi kuwa Sanata Muntari Dan Dutse bayyana ayyukan da ya kawo wa yankin Funtua daga gwmanatin tarayya na cigaban alumma ya yi, da kuma ayyukan da gwamna Umar Dikko Rada ke yi ya sanya jiga-jigan Jamiyyar Adawa ta PDP a Funtua ya amshesu zuwa Jamiyyar APC saboda sun ga aiki a ƙasa ba yaudara ba.
A karshe a madadin 'yan takarar, Shugaban Karamar Hukumar Funtuwa, Hon Abdu Goya ya bayyana godiyar su ga Jamiyyar APC da ta zaɓo su a zaɓen Kananan Hukumomin. "Da yardar Allah idan muka kai gaci, ba za mu ba jama'ar mu kunya ba. Za mu yi koyi da gwamna Umar Dikko Radda wajen ayyukan ci gaban al'umma," in ji shi.

No comments