Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana naɗin da aka yi wa Muhammad Babandede, babban Jami'i a Hukumar hana fasa ƙwabri ta ƙasa na Sara...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An bayyana naɗin da aka yi wa Muhammad Babandede, babban Jami'i a Hukumar hana fasa ƙwabri ta ƙasa na Sarautar Magajin Rafin Hadejia ta jihar Jigawa da cewa abin farin ciki ne ga zuriyar Marigayi Babandede, domin an tabbatar musu da sarautar da suka gada.
Hajiya Amina Muhammad Babandede, wacce ta ke yaya ce ga sabon Magajin Rafin Haɗejia da aka naɗa ce ta bayyana a lokacin da ta ke zantawa da ‘yan jarida a Hadejia cikin makon nan. Inda ta yi nuni da cewa tun farko da aka sanar da su an ba su wannan sarautar, har an bayar da takardar shaid, su ke ta murna da dokin jiran ranar naɗin. Ga shi Allah ya kawo lokacin, ya nuna musu suna godiya ga Allah bisa wannan rana.
Hajiya Amina Muhammad Babandede ta ce su tsakaninsu da jama’a da yin hidima gare su abu ne da suka gada tun daga Madaki Ahmadu zuwa Madaki Sarkiki zuwa Muhammadu Babandede Sarkiki har zuwa kan shi da aka naɗa, kamar yadda mahaifinsu yake yana kwatanta hidima ga al’umma, shi ma suna addu’ar Allah ya ƙara taimakonsu a kan abin da ake a ƙara ci gaba.
Ta ƙara da cewa babu abin da za su ce wa Sarkin Haɗejia, domin abin da ya yi musu na tabbatar da sarautar Magajin Rafi a gidansu, sai dai su yi masa addu’a tun daga kan mahaifinsa har zuwa kansa da ma wata alaƙa ce ƙullalliya tsakanin mahaifinsu da mahaifinsa, har kuma ta zo da shi da babban wansu babban Kwanturolan na hukumar shige da fice mai ritaya Babandede, saboda haka suna addu’a ga Sarki. Yadda suke yi wa iyayensu haka shi ma suke saka shi a ciki.

No comments