Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe Ta Jihar Kano Na Binciken Wasu Ma'aikatan Ƙaramar Hukumar Nasarawa

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Hukumar sauraren ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta  kama wasu ma'aika a Karamar...

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Hukumar sauraren ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta  kama wasu ma'aika a Karamar Hukumar Nasarawa da Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan jihar Kano, Mustapha Maifada bisa zargin karkatar da Naira Miliyan 105.

Ma'aikatan da aka kama sun ƙunshi Daraktan Kula da Ma’aikata, da Ma’ajin kuɗi na Karamar Hukumar. Wata majiya kuma ta ce, an umurci ma'aikatan ne su baiwa Mustapha Maida N105,000,000 domin gudanar da wani shiri, amma sai suka yi kuskuren tura masa Naira Miliyan Ɗari da Biyar,  kamar yadda suka faɗa

Bincike ya nuna cewa a watan Nuwamba ta shekarar 2024, lamarin ya faru shi Mustapha Maifada kawai ya fara amfani da kuɗin da aka aika masa, ake zargin ya sayi kadarori har da mota.

Yanzu haka dai, Hukuma, ƙarƙashin Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado na ci gaba da tsare waɗanda ake zargi domin faɗaɗa bincike kan lamarin.

 

No comments