Daga Musa Muhammad Jim kaɗan bayan kammala sallar Juma'a ta yau ɗin nan a masallacin fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ne shugaban ƙasa B...
Jim kaɗan bayan kammala sallar Juma'a ta yau ɗin nan a masallacin fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ne shugaban ƙasa Bola Ahmad Tibunu ya gana da shugabannin ɗariƙar Tijjaniyya, ƙarƙashin jagorancin Shaikh Mohammadoul Mahi Naiss.
A taron na yau, akwai wakilin Shaikh Ɗahiru Usman Bauchi, wato ɗansa, Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi, babban Limamin masallacin fadar shugaban ƙasar, Imam Abdulwaheed Suleiman, tare da wasu ƙusoshin gwamnatin tarayya.
Mnistan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris da Minista mai kula da harkokin ƙasashen waje, Amb. Yusuff Tuggar, duk suna cikin wannan ganawa.


No comments