Daga Ibrahim Muhammad, Kano Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya jagoranci ƙaddamar da buɗe wata makaranta da ...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya jagoranci ƙaddamar da buɗe wata makaranta da masallaci wanda mataimakin Manajan Daraktan Hukumar KASCO, Hon. Aminu Aminu ya gyara aka ƙaddamar a matsayin khumusi da waƙafi ga mahaifinsu Marigayi Aminu Umar Mai fanfo a Unguwar Kawaji da ke Kano.
Da yake zantawa da 'yan jarida bayan ƙaddamarwa, Hon. Aminu Aminu mai fanfo ya ce dama makarantar da masallacin harsashi ne da mahaifinsa ya dasa, bayan rasuwar sa cikin ikon Allah bayan shekara 20 ya tabbatar da wannan niyya na mahaifinsa, ya gyara makarantar da masallacin domin cika masa niyyar sa.
Ya ce ya gode wa Allah da ƙaddamar da buɗe makaranta da masallacin don cika wa mahaifinsu niyya na tabbatar da wannan makaranta a matsayin kyauta da kuma sakata a matsayin Khumusi da waƙafi ga mahaifin su.
Hon. Aminu Aminu Mai fanfo ya ce sun kafa kwamiti da za su kula da makarantar tare da damƙa ta a hannun Gwamnatin jihar Kano domin mutane su sami sauƙin yin karatu kyauta a makarantar.
Sannan suna da shirin samar da Islamiyya da ƙirƙiro hanyoyi da za a taimaka wa ɗalibai koyon sana'o'i na hannu, kuma za su ci gaba da bayar da duk wata gudumuwa a gwamnatance da kuma nasu na kan su domin ci gaban makarantar.
Hon. Aminu Aminu ya ce yana cikin matuƙar farin ciki na cika wa mahaifinsa wannan niyya da alƙawarin, domin duk wani ɗa so yake ya tabbatar ya zama nagari wajen yin abin alheri ga iyayen sa.
Daga nan sai Hon. Aminu Aminu ya yi kira da cewa ya kamata mutane su riƙa ɗaukar irin wannan ayyuka ya zama abin koyi.

No comments