Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sanata Alƙali Ya Yaba Wa Izala Kan Shirya Musabaƙar Alƙur'ani

 Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ministan Sufuri na tarayya Sanata Ahmed Alƙali ya yaba wa ƙungiyar Izala ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin Sheikh Sa...


 Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Ministan Sufuri na tarayya Sanata Ahmed Alƙali ya yaba wa ƙungiyar Izala ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin Sheikh Sani Yahaya jingir bisa jajircewarta wajen shirya aikin alhairi na ilimi da ilmantarwa, musamman akan abin da ya fi komai muhimmanci a harkar ilimi, shi ne ilimin Alƙur'ani.

Ministan ya yi wannan yabon ne ta bakin babban mataimakansa, Farfesa Shu'aibu Abdullahi Dan Wanka, wanda ya wakilce shi a wajen taron rufe musabaƙar da ƙungiyar ta gudanar a Kano na tsawon mako ɗaya.

Ministan ya ƙara da yi wa ƙungiyar da shugabannin ta da masu hidimta mata fatan alkhari, inda ya jinjina musu da yaba wa ƙwazon dukkan 'yan takara da suka shiga musabaƙar da suka fito daga jihohin ƙasar nan har ma da na Jamhuriyar Nijar da Ghana.

Ministan ya kuma ƙara da cewa a shirye yake ya ci gaba da bayar da gudumuwa a duk wani abu da ya taso a ƙungiyar domin bunƙasa koyarwar addinin musulunci.

Wakilin Ministan, Farfesa Shu'aibu Abdallah Dan'wanka ya bada haƙuri a madadin Ministan na kasancewar ba shi ne ya zo da kansa ba sai wakilci saboda wasu dalilai na aiki da suka taso masa.

No comments