Daga Ibrahim Muhammad, Kano Muna godiya ga mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da ya dube mu ya gadar mana da arzikin iyaye, ta nada mu...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Muna godiya ga mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da ya dube mu ya gadar mana da arzikin iyaye, ta nada mu a wannan Sarauta ta Mai Unguwar Mundubawan Kano
Alhaji Mahmud Aminu Yusu, wanda mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi ya naɗa a matsayin sabon Mai unguwar Mundubawan Kano ne ya bayyana hakan.
Ya ce" ba abin da zan ce da Sarkin Kano sai Allah ya saka masa da alkhairi, domin ita Sarauta idan aka naɗa ka ko da gado ne, sai da soyayya koda za a haife ku ku Dubu ku gada, amma wanda Allah ya sa soyayya da ƙauna da kusanci sai ka ga Allah ya tabbatar masa."
Daga nan ya yi nuni da cewa ita asalin sarautar mai Unguwar Mundubawan Kano, sarauta ce ta ɗaya daga gidajen Fulani ta gidan Modibbon Sulaimanu ne, Sarkin Kano wanda Fulani ne da suka riƙe sarauta a Kano.
Mai Unguwar Mundubawan Kano, Alhaji Mahmud Aminu Yusuf ya ce shi ɗan halak kullum abin da ake so yake yi, tun da Allah ya sa suka gaji iyayensu a wannan sarauta suna nan za su ɗora akan abin da suka yi shekara da shekaru da biyayya ga masarautar Kano da mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi.
No comments