Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

CIKAR KWANKWASO 68: Irin Gudumawar Da Ya Bayar Wajen Ci Gaban Ƙasa -Dk. Wailare

Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana cikar Jagoran Kwankwasiyya, Dk Rabiu Musa Kwankwaso shekaru 68 a matsayin wata baiwa ga al'ummar ...


Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An bayyana cikar Jagoran Kwankwasiyya, Dk Rabiu Musa Kwankwaso shekaru 68 a matsayin wata baiwa ga al'ummar Nijeriya bisa ɗimbin gudumawar da ya bayar ga ci gaban ƙasa. 

Fitaccen mai biyayya ga tsarin manufar siyasar  Kwankwasiyya a Ɗanbatta da Makoɗa, kuma jigo a jam'iyyar NNPP a yankin, Dakta Sale Musa Wailare ne ya bayyana hakan. 

Ya ce jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwasoas jagora ne wanda kullum  yake la'akari da ci gaban da talakawa.

Dakta Wailare, ya ce shekarun Kwankwaso na da mutuƙar fa'ida wajen ci gaban al’ummar jihar Kano, Arewa da ma al'ummar ƙasa baki ɗaya saboda kyakkyawan jagoranci na ra'ayin siyasa da zamantakewa.

Ya ce al'ummar Kano da ƙasa baki ɗaya shaida  ne akan hanyoyin da yake inganta rayuwa jama'a, musamman lokacin da ya yi gwamnan jihar  Kano da matsayinsa ya riƙe a matakin ƙasa har ma a yanzu, da baya riƙe da kowane matsayi.

Dakta Wailare, ya ce Jagora Kwankwaso, ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al'umma  musamman talakawa hidima ta fuskoki  daban-daban musamman a ɓangaren bunƙasa ilimi wanda shi ne ƙashin bayan duk wani ci gaba.

Dakta Sallar Musa Wailare wanda shine ya kafa Gidauniyar ta Malam da yake tallafa wa ci gaban al'umma a Ɗanbatta da Makoɗa ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da baiwa jagoransu na siyasa, Dakta  Kwankwaso tsawon rai da lafiya ya cika masa burinsa don ya ci gaba da taimakon al'ummar jihar da ɗaukacin al'umma zuwa ga ci gaba mai kyau.

No comments