Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ajiyan Kano, Sarkin Fulanin Shanono Alhaji Ja'afar Muhammad Shanono ya ce zai ci gaba da bada gudunmawa kam...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Ajiyan Kano, Sarkin Fulanin Shanono Alhaji Ja'afar Muhammad Shanono ya ce zai ci gaba da bada gudunmawa kamar yadda ya saba a mahaifarsa ta karamar hukumar Shanono wajen hidimta wa jama'a ta fannin ci gaban Ilimi, kiwon lafiya, ruwan sha da sauran abubuwa, waɗanda ya saba yi tun kafin wannan naɗi da aka yi masa.
Sarkin Fulanin ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da 'yan jarida jim kaɗan bayan naɗin da Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi na ll ya yi masa a fadarsa a matsayin sabon Ajiyar Kano.
Ya ce shi ba shi da ta cewa sai godiya ga Sarkin Kano, Khalifan Tijjaniya Muhammad Sanusi saboda dawo musu da wannan Sarautar tasu da ta daɗe ba ta a gidansu, amma ya zama sababin dawowarta gidan.
Alhaji Ja'afar Muhammad Shanono ya ce halayyar sa masu nagarta da Sarkin ya bayyana, ya san su ne saboda yi aiki da mai martaba Sarki Muhammad Sanusi tun yana Gwamnan babban bankin ƙasa a matsayin mataimakinsa na musamman tsawon shekaru Biyar, inda har a halin yanzu kuma shi yana ci gaba da yi wa ƙasa hidima a bankin na ƙasa.
Ajiyan Kano Sarkin Fulanin Shanono, ya kuma bayyana godiya ga jama'a bisa irin dafifin da suka yi na taya shi murna, wanda soyayya ce ta kawo hakan, wanda Allah ya yi wa arzikin mutane sai ya gode wa Allah.
Daga nan ya jaddada godiya ga Allah da masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin Sarki Malam Muhammad Sanusi ta yi, da Hakimai da duk sauran jama'a da suka zo don taya shi murna .
Ita ma ɗaya daga cikin ƙanne kuma shaƙiƙai ga sabon Ajiyan na Kano, Hajiya Hadiza Magaji Buhari ta suna farin cikin ta ne mutuƙa da godiya ga Sarkin Muhammad Sanusi bisa wannan dama da ya ba su.
Ta ƙara da cewa, su sun san Ajiyan Kano mutum ne da yake abubuwa da dama na taimaka al'umma, duk wanda yake shiga Shanono zai ga ximbin ayyukansa, kama daga samar da ruwan sha, makarantu, taimaka wa mata da marayu da sauran fannoni, ba kawai a shanono kaxai ba, da sauran wurare.
Hajiya Hadiza Magaji Buhari ta ce tana da tabbacin ɗan'uwan nata zai ci gaba da hidimar da yake yi ga al'umma, kuma tana baiwa al'ummar Shanono tabbacin sun sami da mai mutunci da kishi na ci gaban su.
No comments