Gabanin zaben ƙananan hukumomi da aka shirya gudanarwa ranar 19 ga watan Oktoba, 2024, a jihar Kaduna, Majalisar Bada Shawarwari a Tsakanin ...
Gabanin zaben ƙananan hukumomi da aka shirya gudanarwa ranar 19 ga watan Oktoba, 2024, a jihar Kaduna, Majalisar Bada Shawarwari a Tsakanin Jam’iyyu (IPAC), reshen Kaduna, ta gudanar da wani taron baje kolin wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a a kan buƙatar yin amfani da katin zabe da kuma zaben ’yan takarar da suke so.
Gangamin da aka gudanar a kan titi wanda aka fara daga titin Katsina Road ya samu halartar jami’an majalisar da kuma jami’an sauran jam’iyyun siyasa.
Jami’an tsaro da kuma jami’an hukumar kiyaye haɗɗura ta tarayya sun hallara domin samar da tsaro tare da jagorantar zirga-zirgar ababen hawa a lokacin gangamin.
An ga Jami’an majalisar ta IPAC suna raba wasu takardu, inda daga ƙarshe suka tsaya a shataletalen filin wasan Kaduna domin tattaunawa da manema labarai kan dalilin da ya sa suka gudanar da bikin baje kolin a kan titi.
Da yake magana a wata hira da shugaban IPAC na Kaduna, Hon. Ahmad Tijjani Mustapha ya bayyana cewa sun gudanar da bikin baje kolin ne domin wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a game da zaben ƙananan hukumomin jihar da aka shirya gudanarwa ranar 19 ga watan Oktoba, 2024.
“Muna kuma son mutane su san muhimmancin yin amfani da ikonsu a lokacin zabe.
"Kun san ƙaramar hukuma ta fi kusa da jama'a kuma ya kamata mutane su sani cewa wajibi ne su zabi 'yan takarar da suke so ba tare da wata tsangwama ba," inji shi.
Shugaban IPAC wanda kuma shi ne shugaban jam’iyyar ADC na jihar ya ce muna wayar da kan masu kada kuri’a da su san muhimmancin zaben da zai ba su damar miƙa kokensu ga jami’an ƙananan hukumomi.
Ya bayyana cewa, “har yanzu hukumar zabe ba ta karkata akalar zaben ba, yana mai cewa ya kamata mutane su fahimci cewa babu wani zabe da ya kai kashi ɗari.
No comments