Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sadaukarwar Jami'an Askarawan Zamfara Da Aka Kashe, Ba Zai Tafi A Banza ba -Gwamna Lawal

Gwamna Dauda Lawal ya yi alƙawarin cewa gwamnatin sa za ta bayar da cikakkiyar kulawa ga iyalan jami'an Askarawan Zamfara da aka kashe a...


Gwamna Dauda Lawal ya yi alÆ™awarin cewa gwamnatin sa za ta bayar da cikakkiyar kulawa ga iyalan jami'an Askarawan Zamfara da aka kashe a wani kwanton É“aunar da aka yi masu. 

Gwamnan ya yi wannan alÆ™awarin ne a fadar 'Yan Doton Tsafe lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan jami'an Askarawan Zamfara da 'yan bindiga suka yi wa kwanton É“auna a cikin makon da ya gabata. 

Yayin jajanta wa masarautar da kuma Iyalan waÉ—anda aka kashen, Gwamna Lawal ya nuna cewa wannan sadaukarwa da jami'an suka yi, ba za ta tafi a banza ba. 

A cikin wata sanarwa da ya fitar yau a Gusau, Mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya ambato Gwamna Lawal yana cewa: "Na zo nan yau ne domin in miÆ™a ta'aziyyata ga masarauta, iyalai da al'ummar Tsafe bisa kisan da aka yi wa gwarazan mu, a wani kwanton É“auna da aka yi masu. 

"Wannan wani bala'i ne wanda muka ji raÉ—aÉ—in sa matuÆ™a. Lallai mun shaida wannan tsayin-daka na waÉ—annan dakaru don kare rayukan al'ummar su. 

"Ina jin wannan baƙin labari, sai na turo da wata ƙaƙƙarfar tawaga ta gwamnati, ƙarshin jagorancin Mataimakin Gwamna domin su zo su miƙa ta'aziyya ga masarauta da iyalan waɗanda abin ya shafa.

"Ina tabbatar maku da cewa irin waÉ—annan abubuwan, ba za su dakatar da mu daga farmakin mu ke kai wa 'yan bindiga ba. Muna yin duk abin da ya wajaba wajen kawo Æ™arshen 'yan bindiga a jihar Zamfara. 

"Gwamnatin jihar Zamfara za ta É—auki duk É—awainiyar iyalan waÉ—annan Asakarawan. Ina yin wannan alÆ™awari ne a nan, kuma za mu tabbatar mun cika shi. 

Nan take kuma Gwamnan ya bayyana bayar da tallafin kuÉ—aÉ—e da kayan abinci ga iyalan mamatan. 

A jawabin da ya gabatar, Sarkin Tsafe, Alhaji Muhammadu Bawa, ya nuna godiyar sa ga Gwamna Lawal, da kuma jijina masa bisa irin namijin ƙoƙarin da ya ke yi wajen samar da tsaro da jin daɗin al'umma.

No comments