Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kotu Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Ɓarayin Da Suka Fasa Banki A Kwara

Mai Shari'a Haleema Salman ta babbar kotun Jihar Kwara, da ke Ilorin ta yanke wa wasu mutum biyar da ake zargi da fasa bankin Offa, huku...

Mai Shari'a Haleema Salman ta babbar kotun Jihar Kwara, da ke Ilorin ta yanke wa wasu mutum biyar da ake zargi da fasa bankin Offa, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

A ranar 5 ga watan Afrilun 2018 ne 'yan fashi suka kai hari bankin a yankin ƙaramar hukumar Offa, inda suka kashe mutum 32 ciki har da 'yansanda tara.

Kotun ta samu mutanen da laifin fashi da makami da kisan mutanen da ba su ji ba su gani ba, ciki har da jami'an 'yansanda a lokacin mummunan harin.

Da farko an tsar yanke hukuncin ranar 2 ga watan Agusta, amma sai aka jinkirta shi sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a faɗin Nijeriya.

No comments