Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kungiyar Shugabannin Majalisun Dokoki Ta Yi Allah-wadai Da Harin Ƙunar Baƙin Wake A Borno

Daga Musa Muhammad, Kaduna Ƙungiyar Shugabannin Majalisun Dokoki Na jihohin Arewacin Nijeriya ta yi Allah-wadai da harin ƙunar baƙin waken d...


Daga Musa Muhammad, Kaduna

Ƙungiyar Shugabannin Majalisun Dokoki Na jihohin Arewacin Nijeriya ta yi Allah-wadai da harin ƙunar baƙin waken da ya kashe aƙalla mutum 18 a garin Gwoza ta Jihar Borno. 

Shugaban ƙungiyar, kuma shugaban Majalisar Dokokin jihar Kaduna, Hon. Ɗahiru Yusuf Liman ya bayyana matuƙar damuwar sa bisa wannan abin takaci, a madadin sauran shugabannin majalisun Dokokin yankin. 

Acikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan harkokin jam’iyyu ga Shugaban ƙungiyar, Malam Mika'ilu Abubakar ya sanya wa hannu a Kaduna Lahadin nan, ta bayyana cewa, "cikin tsananin baƙin ciki ne mu ke nuna damuwa kan mummunan harin ƙunar baƙin wake da ya auku a Ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno.

"A madadin Ƙungiyar Kakakin majalisar Dokokin Arewacin Nijeriya, Hon. Ɗahiru Yusuf Liman, Shugaban Ƙungiyar Kakakin Arewacin Nijeriya kuma Kakakin Majalisar Dokokin Jihar kaduna, muna miƙa saƙon ta'aziyyar mu ga iyalan waɗanda wannan ɗanyen aiki ya shafa da ɗaukacin al'ummar Jihar Borno."

Shugaban ya ce, "harin na rashin hankali, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayukan fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba, tare da raunata wasu da dama, babban abin takaici ne a kan ƙalubalen tsaro da ƙasar mu ke fuskanta.

"Wannn hari ne ba kawai ga mutanen Gwoza kaɗai ba, har ma a kan dukkan al’ummar mu.

"Mun yi Allah-wadai da wannan ta'addanci da kakkausar murya, tare da tsayawa tsayin-daka da al'ummar jihar Borno a wannan mawuyacin lokaci.'

Ƙungiyar ta yaba da yadda jami’an tsaro suka mayar da martani cikin gaggawa, tare da kira gare su da cewa kada su huta har sai an gurfanar da waɗanda suka aikata wannan ta’asa a gaban kotu.

"Ya zama wajibi a ɗauki dukkan matakan da suka dace domin daƙile irin waɗannan hare-hare a nan gaba da kuma tabbatar da tsaron ’yan ƙasa."

Bugu da ƙari, ƙungiyar ta kuma yi kira ga dukkan matakan gwamnati da su ƙara zage damtse wajen tunkarar matsalolin ta'addanci da tashe-tashen hankula a yankin mu da ma ƙasa baki ɗaya.

Ta ce, "yana da matuƙar muhimmanci a samar da zaman lafiya, haɗin kai, da ci gaba a matsayin ginshiƙan tabbatar da tsaro da zaman lafiyar Nijeriya mai albarka."

"Yayin da muke alhinin rashin 'yan uwan mu 'yan Nijeriya, ya kamata mu tuna da ƙarfin da ya bayyana mu a matsayin al’umma. Tare, za mu shawo kan waɗannan ƙalubalen kuma mu gina makoma ba tare da tsoro da tashin hankali ba.

"Allah ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu, Ya sa sun huta, Ya bai wa waɗanda suka jikkata lafiya.

"Za mu ci gaba da addu'o'i ga iyalai da masoyan waɗanda abin ya shafa," in ji ƙungiyar.

No comments