Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Tallafa Wa Mata 'Yan Kasuwa

Daga Hussaini Yero, Gusau A ƙoƙarin ta na tallafa wa Mata domin su dogara da kansu. Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda La...

Daga Hussaini Yero, Gusau

A ƙoƙarin ta na tallafa wa Mata domin su dogara da kansu. Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta nuna bajinta wajen bayar da tallafi Naira Miliyan Ɗaya ga wasu mata ‘yan kasuwa don dogaro da kansu da kuma kauce wa shiga muguwar hanyar ta ba ta dace ba, ya sanya ta ba su talkafin kasuwanci.

Mataimakiyar Uwar gidan Gwamna Dauda Lawal  akan yaɗa labarai da Sadarwa, Zahara'u Musa ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta sanya wa hannun ga manema labarai a Gusau.

"Wannan matakin ya yi daidai da ƙudirin gwamnatin Dauda Lawal a halin yanzu na jajircewar sa wajen baiwa mata damar dogaro da kai don bayar da gudunmawa mai tsoka wajen kyautata ma iyalansu da kuma ci gaban jihar.

Hajiya Huriyya Dauda ta jaddada muhimmancin da ake baiwa mata wajen ƙarfafa masu. Kuma gwamnatin Dauda Lawal ta gina cibiyoyin koyon sana’o’i guda uku a mazaɓun ‘yan Majalisar Dattawa uku.

Uwar gidan Gwamnan jihar ta bayar da gudunmawar kuɗi Naira Miliyan Ɗaya a matsayin Gudummawar jari ga su "'yan Kasuwar.

Daga nan Hajiya Huriya ta yi kira ga waɗanda suka amfana da su kasance abin koyi ga sauran mata, musamman wajen yin sana'a da tallafin kuɗin.

Daga ƙarshe ƙungiyar mata 'yan kasuwa sun kararma ta da muƙamin 'Jagabar Mata 'Yan Kasuwa.'

 

No comments