Daga Ibrahim Muhammad, Kano Shugaban kwalejin Ilimi ta Aminu Kano da jihar Kano, Daktar Ayuba Ahmad ya roƙi gwamnatin jihar da ta talla wa K...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Shugaban kwalejin Ilimi ta Aminu Kano da jihar Kano, Daktar Ayuba Ahmad ya roƙi gwamnatin jihar da ta talla wa Kwalejin da fili domin ta kafa Jami'a.
Shugaban ya yi wannan roƙo ne a lokacin da yake gabatar a wani taron bayar da Shaida ga ɗaliban da suka kammala karatun NCE a Kwalejin .
Dr Ayuba ya nuna cewa yanzu duk wanda ya wuce ta zagayen harabar Kwalejin zai tsammaci suna ba da shaidar karatun Digiri ne.
Ya ce saboda a wannan harabar suna da zauruka dabandabn na koyo da koyarwa kusan bakwai, suna ɗaukar sama da ɗalibai 1,000.
Dakta Ayuba ya ce a ƙoƙarin da suke yi na tallafa wa bunƙasar ilm, Kwalejin na shirin bayar da tallafin karatu ga ɗalibai 1,000 'yan asalin jihar Kano.
A jawabin sa, Kwamishinan ilimi Mai zurfi na jihar Kano, Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ya ce gwamnatin jihar, a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta baiwa harkar ilimi kulawa ta musamman saboda muhimmancin sa wajen ciyar da kowace al’umma gaba.
Dakta, Kofar Mata wanda shi ne ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf a wajen bikin yaye ɗaliban, ya yaba da ƙoƙarin Kwalejin wajen bunƙasa ilimi.
No comments