Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ya Kamata Nijeriya Ta Fara Kiwon Macizai Don Samun Kuɗin Shiga -Idris Mai Macizai

Daga Musa Muhammad, Kaduna Wani shahararren mai sana'ar kamawa da kiwon macizai, kuma Ɗan jarida a garin Samarun Zariya da ke jihar Kadu...

Daga Musa Muhammad, Kaduna

Wani shahararren mai sana'ar kamawa da kiwon macizai, kuma Ɗan jarida a garin Samarun Zariya da ke jihar Kaduna, Malam Idrid Umar ya jawo hankalin gwamnatocin jihohi da na tarayya kan su shiga kiwon macizai, wanda ya ce hakan zai taimaka masu wajen samun kuɗaɗen shiga. 

Tun farko a tattaunawar su da wakilin mu, Malam Idris ya bayyana yadda yake rayuwa da macizai a gidan sa, dare da rana. 

Daga nan masanin harkar macizan ya ba gwamnatin Nijeriya da na jihohi shawarar da su ƙirƙiro da hanyar da za a fara kiwon macizai a gwamnatance, ba tare da wani tsoro ba.

Masanin ya ce, bincike ya nuna cewa har yanzu ba a sami wani ma'adani da Ya kai dafin maciji daraja ba a kasuwance a duniya baki ɗaya.

Ya ce, daga cikin baiwar da Allah ya yi wa maciji, shi maciji ba ya wab, wato bai cika saurin mutuwa kamar yadda sauran dabbobi suke yi ba. Ya ce, sannan maciji ya na saurin yaɗuwa, domin ya kan yi ƙwai guda ɗari (100) a lokaci guda, kuma ya ƙyanƙyashe su baki ɗaya.

Da ya ke bayyana sirrorin da dafin maciji ke da su, waɗanda ɗan adam ke amfani da su a rayuwa kuwa, Malam Idris ya nuna cewa ana amfani dafin maciji wajen haɗa manyan makamai da ake amfani da su a duniya, musamman (makaman ƙare dangi) da ake yaƙe-yaƙe da su, duk da dafin maciji ake haɗa sinadaran.

Sannan ya ce ana harhaɗa magunguna kala-kala da dafin maciji, musamman cututtukan da suka shafi Kansa.

Malamin ya tabbatar da cewa dukkan matsalar da ake samu na rasa rayuka a jihohi kamar jihar Gombe a Kaltungo da Billiri a jihar Filato sakamakon cizon macizai, wanda da gwamnati ta faɗaɗa tunani akan kiwon macizai, da an sami sauƙin matsalar da ke addabar mutanen yankin.

Ya ce dalili shi ne, ita allurar da ake yi wa duk wanda maciji ya sara ko ya caka, to a duk faɗin duniya da Dafin maciji ake haɗawa a kimiyyar zamani ta duniya.

Malamin ya ce, yanzu haka a ilmin kimiyya, kowane maciji idan ya yi cizo, da irin allura da ake yi wa mutum, domin kowane maciji da irin allurar sa.

Ya ce, amma tambaya anan shine idan maciji yayi cizo a cikin dare bayan yayi cizon sai ya gudu ya za ayi da wanda macijin ya ciza? 

Ga shi a doka ba zai yiwu baƙin maciji ya yi cizo, sai Likita ya yi ma mutum allurar da ba ta baƙin maciji ba, wanda kuma hakan haɗari ne babba.

Saboda haka sai Malam Idris ya bayar da shawacewa, yana da muhimmanci gwamnati ta fito da hanyar faɗaɗa kiwon macizai, wanda hakan zai sa a sami ƙwararrun Likitoci a fannin da za su   iya ƙirƙiro magunguna daban daban-daban da za su taimaka wa al'ummar ƙasa baki ɗaya.

Ya ci gaba da cewa, idan gwamnati ta fara kiwon macizai, za ta sami kuɗaɗen shiga mai tsoka, domin dafin maciji ya fi zinari tsada a kasuwar duniya.

Masanin macizan ya kuma nuna takaicin sa game da binciken da ya nuna cewa ana asarar rayuka da dama a asibitoci da gidaje bisa rashin maganin cizon macizai, wanda ya ce ya kamata gwamnati ta fito hanyoyin samun magungunan. 

Daga nan ya yi tilawar cewa alokacin gwamnatin Marigayi Janar Sani Abacha an sami ci gaba, inda gwamnatin sa ta fitar da wani tsarin haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da ƙasar Ingila, inda aka fitar 'ba ni gishiri, in ba ka Manda.'

Wato Nijeriya na baiwa Ingila macizai, su kuma sai su ba Nijeriya magungunan da suka haɗa da dafin macizan. A yi wannan yarjejeniya ce a ƙarƙashin Ma'aikatar lafiya ta tarayya. Wanda kuma wannan shiri ya taimaki al'ummar Nijeriya matuƙa.





No comments