A wani abu da ake ganin kamar zai tayar da babbar fitina a Kano, Sarki Muhammadu Sanusi da Sarki Aminu Ado Bayero sun sha alwashin gabatar d...
A wani abu da ake ganin kamar zai tayar da babbar fitina a Kano, Sarki Muhammadu Sanusi da Sarki Aminu Ado Bayero sun sha alwashin gabatar da Lamancin sallar Juma'a a masallacin Fada, kamar dai aka saba Sarkin Kano na yi.
Ana sa ran Sarki Sanusi II, wanda yanzu haka shi ke zaune a Fadar Sarkin Kano, wacce ta ke kusa da masallacin Juma'ar, shi ne zai fito domin jagorantar sallar Juma'ar.
"Sarki Sanusi II ne zai jagoranci sallar Juma'a a masallacin Fada a matsayin sa na Sarki," kamar yadda ya ke ƙunshe cikin wata sanarwa jiya Alhamis da daddare.
A sanarwar, wacce ke É—auke da sa hannun ÆŠanburan Kano, Munir Sanusi Bayero, ya bayyana cewa lallai babu makawa Sarki Sanusi II zai jagoranci sallar Juma'a a masallacin Fada.
Don haka sai ÆŠanburan ya yi kira ga al'ummar Kano su tuÉ—aÉ—o zuwa masallacin Fadar domin sauraren huÉ—ubar Juma'a daga bakin Sarki Sanisi II.
A wata sabuwa kuma, cikin wata sanarwa da É—aya daga cikin masu taimaka wa Sarki Aminu Ado Bayero ya fitar, ya nemi al'ummar Kano su mara wa Sarki Aminu baya don halartar sallar Juma'a a masallacin na Fada.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa tun da misalin ƙarfe 12:30 na rana ne za a fara shirye-shiryen tafiyar Sarkin, daga ƙaramar Fada ta Nasarawa zuwa babban masallacin da ke Fada, wacce 'yan kilomitoci ne a tsakani.
Ya zuwa haɗa labarin nan dai, ana sauraron ta ɓangaren jami'an tsaro game da wannan dambarwa.
No comments