Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sabon Tasku Ga Tsohon Gwamnan Kogi: Hukumar Shige da Fice Ta Sanya Shi Cikin Waɗanda Ta Sa Wa Jan Layi

  Bayan da Hukumar EFCC ta bayyana cewa tana neman Tsohon Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ruwa-a-jallo, sai ga shi kuma a jiya Hukumar shige...

 

Bayan da Hukumar EFCC ta bayyana cewa tana neman Tsohon Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ruwa-a-jallo, sai ga shi kuma a jiya Hukumar shige da fice ta 'Nigeria Immigration Service (NIS), ta shelanta cewa ta sanya Tsohon Gwamnan a jerin sunayen waɗanda ta sa wa ido don kar ya sulale ya bar ƙasar.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwar Hukumar mai lamba NIS/HQ/IAC/INV/15621, mai ɗauke da kwanan wata 18 ga Afrilu, 2024, wacce Mataimakin Kwantirola mai kula da sashen waɗanda ake zargi, DS Umar ya rattaba wa hannu.

Sanarwar ta ce, an sanar da Shugaban Hukumar tsaron farin kaya ta DSS, Shugaban 'yan sandan Nijeriya, Shugaban Hukumar tsaro ta ƙasa da ƙasa ta NIA da duk rassan Hukumar ta shige da five da ke faɗin ƙasar nan game da wannan mataki.

Haka kuma sanarwar tana ƙunshe da lambar Fasfo ɗin Tsohon Gwamnan kamar haka; B50083321, Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello. “An umurce ni da in sanar da ku cewa wannan mai suna a sama, yanzu yana cikin jerin sunayen waɗanda aka sanya wa ido."

“Muna sanar sa ku cewa wannan da ake zargi, wata babbar kotun tarayya a Abuja ta gurfanar da shi bisa zargin haɗa baki, zamba cikin aminci da mallakar kuɗaɗen da ba na halali ba," in ji sanarwar. 

No comments