Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar Shugabannin Jam'iyyun Siyasar Arewa Ta Yaba Wa Gwamnan Kaduna Kan Sako Ɗaliban Kuriga

Daga Musa Muhammad  Ƙungiyar Shgabannin Jam'iyyun Siyasa ta Arewan Nijeriya ta miƙa godiya ta musamman da gingina ga Gwamnan Jihar Kadun...


Daga Musa Muhammad 

Ƙungiyar Shgabannin Jam'iyyun Siyasa ta Arewan Nijeriya ta miƙa godiya ta musamman da gingina ga Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani bisa gaggarumin ɗaukar mataki na ganin an sako ɗaliban da ’yan bindiga suka sace a Kuriga.

A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kaduna, Babban Sakataren Ƙungiyar Mall Mikailu Abubakar ya ce, sace ɗaliban wani lamari ne mai ban tsoro da ya girgiza al’ummar jihar da ma ƙasar baki ɗaya. To sai dai yadda Gwamna Uba Sani ya jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya da walwalar al’ummar Jihar Kaduna, ya fito fili a ƙoƙarin da ya yi na kuɓutar da ɗaliban.

Malam Mikailu Abubakar ya yaba da yadda gwamnan ya gaggauta tattara jami’an tsaro da kayan aiki, ya ce "tare da jajircewarsa sun taka rawar gani wajen ganin an dawo da ɗaliban da aka sace cikin ƙoshin lafiya. Yunƙurin da ya yi da kuma jajircewarsa wajen yaƙar ta’addanci ya sanya wa al’ummar Jihar Kaduna nutsuwa da kuma ƙwarin gwiwa."

"A matsayinmu na wakilan jam’iyyun siyasa daban-daban na yankin Arewa, muna yaba wa Gwamna Sen Uba Sani bisa kyakkyawan jagoranci da ɗaukar matakin da ya dace kan wannan al’amari. Ƙarfinsa na hada kan masu ruwa da tsaki daban-daban da haɗa kai don cimma manufa guda abin yabawa ne kuma ya zama shaida na sadaukar da kai ga jin daɗun jama'a," in ji Abubakar.

Ya ce, "muna miƙa godiyarmu ga Gwamna Uba Sani da tawagarsa bisa namijin ƙoƙarin da suka yi wajen ganin an sako ɗaliban Kuriga da aka yi garkuwa. Ayyukan da suka yi ba wai kawai ceton rayuka ba ne, har ma ya nuna yadda gwamnati ta himmatu wajen kare al’ummarta da kuma tabbatar da bin doka da oda."

"Ƙungiyar Shugabannin Jam'iyyun Siyasar Arewa tana goyon bayan Gwamna Uba Sani ɗari bisa ɗari tare da yin alƙawarin ci gaba da bayar da goyon baya wajen gina Jihar Kaduna mai albarka", in ji Mikailu.

No comments