Daga Hussaini Yero, Funtua A ƙoƙarin da gwamnatin Jihar Zamfara ke yi na sauƙaƙa ma al'ummar jihar a ƙarshin Ofishin Uwar gidan Gwamnan,...
Daga Hussaini Yero, Funtua
A ƙoƙarin da gwamnatin Jihar Zamfara ke yi na sauƙaƙa ma al'ummar jihar a ƙarshin Ofishin Uwar gidan Gwamnan, Hajiya Huriya, ta ƙaddamar da bada tallafin abincin Azumi da kayan Sallah ga Magidanta dubu ashiri a faɗin jihar.
Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta ƙaddamar da rabon kayan ne a cikin wannan wata na Ramadan a Ƙananan Hukumomin Gummi, Bukkuyum, Anka,Talata Mafara, Bakura Da Maradun.
Kayan abincin da aka raba sun haɗa da Shinkafa, Gero, Masara, Suga, Taliya, Wake, Man gyaɗa da dai sauran su.
Uwargidan Gwamnan ta bayyana cewa, gidaje dubu ashirin ne za su ci gajiyar tallafin a faɗin Ƙananan Hukumomi goma sha huɗu.
Daga nan Uwargida Huriyya ta yi kira ga masu rabon kayan da su ji tsoran Allah wajen rabawa, kuma duk wanda aka samu da ɓata tsarin rabon, lallai zai gamu da hukunci daidai da abin da ya aikata.
Ta kuma buƙaci al’ummar jihar da su yi amfani da wannan lokaci na Azumin Ramadan wajen gudanar da addu’o’i Allah ya ba da ikon kawo ƙarshen wannan hali da aka samu kai a ciki.
Kuma ta tabbatar da cewa, Mai gidanta Gwamna Dauda yana iyaka ƙoƙarisa na sauke haƙƙin da ke kansa na wannan al'umma, musamman samar da tsaron rayuka da dukiyar jama'a.
A nasa jawabin, Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Masarauutu, Hon Ahmad Garba Yandi ya tabbar da cewa wannan tallafin Abincin Azumi da kayan Sallah na daga cikin alƙawuran wannan gwamati a lokacin yaƙin zaɓe
Ya ƙara da cewa, "duk wata gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda muna raba magunguna ga Asibitocin Ƙananan Hukumomi Goma Sha Huɗu da muke da su, kuma kyauta ne ake badawa ga mata da ƙananan yara."
"Akan haka ne Hon. Yandi ya ƙara jaddada cewa, wannan gwamati na da shirye-shirye ga al'ummar Jihar Zamfara na ci gaba. Yanzu dai fatar mu, ita ce Allah ya dafa mana mu cimma burin mu na ciyar da Jihar mu gaba ta kowane fanni.
No comments