Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jami'ar Al-qalam Ta Tabbatar Da Sace Wasu Ɗaliban Ta

Daga Musa Muhammad Jami'ar Al-Qalam da ke Katsina ta tabbatar da batun sace wasu ɗaliban ta biyu. Kimanin kwanaki uku ke nan da faruwar ...

Daga Musa Muhammad

Jami'ar Al-Qalam da ke Katsina ta tabbatar da batun sace wasu ɗaliban ta biyu. Kimanin kwanaki uku ke nan da faruwar lamarin, kafin Jami'ar ta fitar da wannan tabbatarwar, inda ta ce a hanya ne lamarin ya faru, ba a harabar Jami'ar ba. 

A cikin wata sanarwa da Jami'ar ta fitar a yau Alhamis ɗin nan, ta bayyana cewa duk da cewa har yanzu babu cikakken bayani kan yadda aka yi garkuwa da ɗaliban, amma iyayen su sun tabbatar da sace su a lokacin da suke kan hanyar su ta komawa makaranta daga jihar Neja.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne labarin garkuwa da ɗaliban ya karaɗe shafukan sada zumunta ƙasar nan, a daidai lokacin da ake jimamin kisan da masu garkuwa da mutane suka yi wa wata budurwa da suka ɗauke a yankin Abuja.

 

No comments