A ranar Asabar ne Gwamna Dauda Lawal na jijar Zamfara ya ƙaddamar da rabon wasu muhimman kayan noma da kayan amfanin gona ga manoman yanki...
A ranar Asabar ne Gwamna Dauda Lawal na jijar Zamfara ya ƙaddamar da rabon wasu muhimman kayan noma da kayan amfanin gona ga manoman yankin Zamfara ta Yamma, tare da ƙaddamar da ginin makarantar Tsangaya a Gummi.
Bikin ƙaddamarwar, wani ɓangare ne na shirin farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya da annobar Korona ya karya a ƙarƙashin shirin FADAMA III.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce Gwamna Lawal ya ƙaddamar da rabon kayan noma ne tare da gina makarantar Tsangaya ta zamani da ta dace a Ƙaramar Hukumar Gummi.
A cewar sa, gwamnatin jihar ta amince da gina makarantar Islamiyya ta Tsangaya ta zamani a kowace shiyya cikin shiyyoyi uku domin inganta ilimi a Zamfara.
Shirin a Ƙaramar Hukumar Gummi na da nufin samar da muhimman tallafi da ayyuka ga manoman shiyyar Zamfara ta Yamma.
Da yake gabatar da jawabin sa a wajen ƙaddamar da shirin, Gwamna Lawal ya ce an sadaukar da aikin ne domin ginawa, tare da gyara hanyoyin shiga yankunan karkara.
“Gwamnati na za ta tabbatar da gyarawa da gina kasuwanni domin sana'o'i lafiya kuma cikin inganci.
“Babban manufar mu ita ce inganta noma ta hanyar samar wa manoma da muhimman abubuwa, kamar takin zamani, maganin ciyawa, maganin ƙwari, iri masu inganci, da sinadarai masu sanya iri ya yi kyau.
"A lokacin rani mai zuwa, mun ware buhunan taki guda 33,000 – wanda ya ƙunshi buhunan takin NPK 22,000 da kuma buhunan Urea 11,000. Wannan ƙari ne kan noman zamani sama da 700 da iri na noman shinkafa da masara, wanda za a raba wa manoma 19,000. Ƙungiyoyi ɗari bakwai da talatin da biyar na manoma goma, kowanne za a ba su ƙarfin noman zamani, yayin da mutane 2,550 kuma za su karɓi ƙananan dabbobin domin su taimaka masu wajen aiki.”
A yayin ƙaddamar da shirin makarantar Islamiyya ta Tsangaya kuwa, Gwamna Lawal ya tabbatar wa al’ummar yankin mazabar Zamfara ta Yamma cewa makarantar za ta cika ƙa’idoji masu inganci.
No comments